Shugaba Bola Tinubu ya yi wasu muhimman naɗe-naɗen muƙamai, wanda a cewar mai ba shi shawara kan kafafen yaɗa labarai Ajuri Ngelale, sabbin naɗe-naɗen zai ƙara haɓaka ma’aikatu da kwamitocin gwamnati daban-daban.
Ga jerin sunayen waɗanda aka naɗa da mukamansu:
Mr. Silas Agara
Darakta Janar na Hukumar Samar da Aikin Yi ta Kasa (NDE)
Mr. Umar Ibrahim Mohammed
Darakta Janar na Hukumar Kula da Hidimar Ruwa ta Najeriya (NIHSA)
Baffa Dan Agundi
Darakta Janar na Cibiyar Inganta Aiki ta Ƙasa (NPC)
- Shugaba Bola Tinubu Zai Yi Sauye-Sauye A Gwamnatinsa Kwanan nan
- Shugaba Bola Tinubu Ya Naɗa Sanata Bashir Lado Mai Ba Shi Shawara
Cornelius Oluwasegun Adebayo
Sakataren Zartarwa/Kwamishina na Hukumar Raya Filayen Noma ta Kasa (NALDA)
Mr. Saleh Abubakar
Darakta Janar na Hukumar samar bishiyoyi kore hamada (NAGGW)
Dr. Olufemi Adekanmbi
Ko’odinetan tsaftace dagwalon iskar (HYPREP)
Mr. Tosin Adeyanju
Sakataren Zartarwa na Asusun kiyaye dokokin caca na Kasa (NLTF)
Oluwaseun Faleye
Manajan Darakta/Kwamishina na Hukumar Bada Tallafin Inshorar Jama’a ta Najeriya (NSITF)
Mrs. Mojisolaoluwa Kehinde Alli Macaulay
Daraktar Zartarwa (Harkokin Aiki) na Hukumar Bada Tallafin Inshorar Jama’a ta Najeriya (NSITF)
Ms. Omolola Bridget Oloworaran
An bada sunanta a matsayin Darakta Janar na Hukumar Fansho ta Ƙasa (PenCom) (Naɗin yana buƙatar amincewar Majalisar Dattawa)
Mr. Jobson Ewalefoh
An bada sunansa a matsayin Darakta Janar na Hukumar Kula da Jari-Hujja (ICRC) (Naɗin yana buƙatar amincewar Majalisar Dattawa)