Masana da dama na tarayyar Najeriya, sun bayyana muhimmancin fadada musaya tsakanin al’ummun Sin da na Najeriya, ta hanyar karfafa hadin gwiwa a fannonin musayar al’adu, da yawon bude ido karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ko BRI.
Masanan sun bayyana hakan ne yayin wani taron karawa juna sani da ya gudana a ranar Juma’a, game da yayata musayar al’adu, da yawon bude ido karkashin hadin gwiwar shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, suna masu kira da a karfafa hadin gwiwar sassan biyu a bangarorin musayar ilimi, da al’adu da yawon shakatawa.
- Za A Ci Gaba Da Daukar Shirin ‘The Mandate’ A Kasar Faransa – Ezinne Agwu
- ‘Yancin Kananan Hukumomi: Majalisa Na Shirin Hana Bai Wa Gwamnoni 21 Kason Kudinsu Na Tarayya
Da yake tsokaci yayin taron, Mista Biodun Ajiboye, shugaban hukumar fadakar da jama’a game da raya al’adu a Najeriya, ya ce, shawarar BRI ta samar da wata babbar dama ta gudanar da musaya, wanda za ta baiwa kasashen duniya daban daban damar musayar al’adu masu daraja da suka gada da sauran sassan duniya, kana su iya rungumar mabambantan al’adu na abokan cudanyarsu.
Mista Ajiboye ya kara da cewa, Najeriya na da tarin mabambantan kabilu, da harsuna, da al’adu, don haka a shirye take ta shiga a dama da ita, a fannonin musayar al’adu mai ma’ana tare da kasar Sin.
Yayin taron, shi ma jami’in lura da al’adu a ofishin jakadancin Sin dake Najeriya Li Xuda, ya ce shawarar BRI ta yi matukar hore damar zurfafa musaya tsakanin Sin da Najeriya cikin shekaru 6 da suka gabata, tun bayan da Najeriya ta shiga shawarar a shekarar 2018. (Saminu Alhassan)