• English
  • Business News
Tuesday, July 1, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Za A Ci Gaba Da Daukar Shirin ‘The Mandate’ A Kasar Faransa – Ezinne Agwu

by Sulaiman and Rabilu Sanusi Bena
12 months ago
in Nishadi
0
mandate
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Masana’antar Nollywood tana gab da shaida wani gagarumin ci gaba, a yayin da Dakta Princess Ezinne Agwu, sabuwar mai shirya fina-finai a masana’antar Nollywood, ta kammala shirin fim na farko na miliyoyin nairori mai suna, “The Mandate,” a birnin Paris na kasar Faransa.

Dakta Ezinne, wacce ta canza sana’a daga mai shari’a ta kasa da kasa zuwa harkar fim, ta hada kai da fitaccen daraktan Nollywood, Ike Nnaebue domin kawo wannan wasan kwaikwayo a idon duniya.

  • Lamunin Naira Biliyan 5 Ga ‘Yan Fim: Yaushe Kannywood Za Ta Samu Nata?
  • Ali Nuhu Ya Gabatar Da Lacca Kan Fina-finan Nijeriya A Faransa

Ike Nnaebue, wanda ya dawo harkar fina-finai na barkwanci bayan nasarar shirinsa na “No U-Turn,” shi ne darakta a wannan shiri wanda ake fatan idan an kammala shi ya zama irinsa na farko da wani dan Nijeriya ya taba shiryawa. Wannan fim din ya janyo wa Dakta Ezinne yabo mai yawa da suka hada da jinjinan ‘Jury Berlinale’ da kyaututtuka daga kwalejin fina-finan Afirka da bikin fina-finai na duniya na Durban.

Da yake magana game da fin din “The Mandate” da hadin gwiwarsa tare da Dakta Ezinne, Ike ya ce wannan buri ne na kowane mai shirya fina-finai, domin yin aiki mai nagarta tare da samar da fasaha mai muhimmanci.

Ya ce fim din “The Mandate” labari ne na jarumtaka a cikin duniyar da tsoro ya zama aikin yau da kullun.

Labarai Masu Nasaba

Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda

Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)

Majiyoyin da ke kusa da ‘Royalty Life Studios’, inda Dakta Ezinne ke aiki a matsayin shugaba, sun nuna cewa kasafin kudin fim din ya wuce naira miliyan 700.  Sai dai Dakta Ezinne ta ki tabbatar da ainihin alkaluman, inda ta ce, “Ba a gama fim din ba tukuna, za mu bayyana kasafin kudin fim din idan an kamala shi.

Labarin fim din ya nuna yadda Dakta Ezinne Egbuna, Darakta-Janar na Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, wanda ke kalubalantar halin da ake ciki a fagen siyasar Nijeriya da maza suka mamaye.

A yunkurinta na yaki da cin hanci da rashawa da bunkasar ci gaba, ta yi murabus daga mukaminta mai daraja ta tsaya takarar gwamna a karkashin jam’iyyar DPC, karkashin jagorancin Hon.  Lucas Amadi, wanda yake fuskantar adawa mai zafi daga DPA da makiya na boye a cikin jam’iyyar tasa.

Fim din ya kunshi fitattun jaruman da suka hada da Femi Adebayo, Deyemi Okanlawon, Ali Nuhu, Kalu Ikeagwu, Okey Bakasi, Sarauniya Dimma Edochie, Chioma Nwoha da kuma gabatar da sabon jarumi, Peter Ngene.

Dakta Ezinne ta jaddada cewa shawarar da aka yanke na gudanar da ayyukan bayan fage a birnin Paris ya yi daidai da hangen nesanta na samar da labarun gida tare da jawo hankalin duniya.

Ta ce, “Mun himmatu wajen bayar da labarun gida ga masu sauraron duniya,” in ji ta.

Yayin wani taron manema labarai a Abuja za a sanar da cikakkun bayanai kan shirin fitar da fim din da kwanan wata.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Lokaci Ya Yi Da Nijeriya Za Rika Fitar Da Manja Kasashen Waje – Kungiyar Dalibai

Next Post

Sabbin Naɗe-Naɗe 10 Da Shugaba Tinubu Ya Yi Jiya

Related

Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda
Nishadi

Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda

2 days ago
Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)
Nishadi

Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)

1 week ago
Rashin Abinci Na A Waka Ya Sa Na Daina Yi -T Y Shaba
Nishadi

Rashin Abinci Na A Waka Ya Sa Na Daina Yi -T Y Shaba

3 weeks ago
Yadda Jarumai A Masana’antar Kannywood Ke Auren Junansu
Nishadi

Yadda Jarumai A Masana’antar Kannywood Ke Auren Junansu

4 weeks ago
Ban Dauki Harkar Fim Da Wasa Ba -Hauwa Ayawa 
Nishadi

Ban Dauki Harkar Fim Da Wasa Ba -Hauwa Ayawa 

1 month ago
Hukuma Ta Dakatar Da Haska Fina-Finai 22 Har Sai Baba Tagani
Nishadi

Hukuma Ta Dakatar Da Haska Fina-Finai 22 Har Sai Baba Tagani

1 month ago
Next Post
Sabbin Naɗe-Naɗe 10 Da Shugaba Tinubu Ya Yi Jiya

Sabbin Naɗe-Naɗe 10 Da Shugaba Tinubu Ya Yi Jiya

LABARAI MASU NASABA

Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC

Haɗakar Jam’iyyun Adawa Ba Ya Ɗaga Mana Hankali – Sabon Shugaban APC

July 1, 2025
Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

Sin Na Fatan More Fasahohi Da Kirkire-kirkire Da Kasashen Duniya Don Sa Kaimi Ga Ci Gaba Da Zamanintar Da Kasashen Duniya

June 30, 2025
Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano

June 30, 2025
Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu

June 30, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19

June 30, 2025
Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

June 30, 2025
Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina

June 30, 2025
Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

Alkaluman PMI Na Sin Na Bunkasa Cikin Watanni 2 A Jere

June 30, 2025
CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata

June 30, 2025
Sin Ta Kammala Aikin Agajin Gaggawa A Yankin Da Ambaliyar Ruwa Ta Afku

Sin Ta Kammala Aikin Agajin Gaggawa A Yankin Da Ambaliyar Ruwa Ta Afku

June 30, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.