• English
  • Business News
Sunday, October 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yan Kasuwan Ketare Za Su Samu Sabbin Damammaki A Kasar Sin

by Sulaiman and CGTN Hausa
1 year ago
Kasuwa

Alkaluman hukumar kididdaga ta kasar Sin (NBS), sun nuna a yau Litinin cewa, yawan GDPn kasar Sin ya karu da kaso 5% a farkon rabin shekarar nan ta 2024, idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. Kaza lika karuwar samar da kayayyaki ba tare da tangarda ba, da karuwar bukatu ba tare da tsayawa ba, da saurin ci gaban sana’o’i masu alaka da fasahohin zamani da dai sauransu, duk sun nuna cewa tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da farfadowa. 

Ci gaban tattalin arzikin kasar Sin mai inganci ya samarwa kamfanonin kasa da kasa sabbin damammaki. Yanzu haka, kasar Sin na rubanya kokarin raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da zurfafa sabunta masana’antu, ta yadda sana’o’i masu alaka da fasahohin zamani za su bunkasa cikin sauri.

  • Gdpn Sin Ya Karu Da Kashi 5% A Watanni Shida Na Farkon Bana
  • Fahimtar Manufar Kasar Sin Ta Yin Kwaskwarima A Sabon Zamani ——Za A Cimma Buri Idan Aka Kyautata Aiki Bisa Yanayi, Za A Samu Ci Gaba Idan Aka Kiyaye Yin Kirkire-kirkire

A farkon rabin bana, saurin karuwar kudin da aka samu daga sana’ar kere-kere bisa fasahohin zamani, da kuma saurin karuwar jarin da aka zuba a sana’ar dukkansu sun karu matuka. Kana yawan hajojin zamani da ake samarwa ba tare da gurbata muhalli ba, kamar su mutum-mutumin inji masu ba da hidima, da motoci masu amfani da sabbin makamashi, ya karu fiye da kaso 10%. Ana raya masana’antu zuwa na zamani kuma ba tare da gurbata muhalli ba.

Har ila yau, darajar motoci, da jiragen ruwa, da kananan kayayyakin laturoni na “Integrated circuit” da sauransu, wadanda Sin ta sayar ga ketare sun karu matuka a farkon rabin shekarar ta bana, lamarin da ya kara azama kan kyautatuwar tsarin cinikayyar kasa da kasa na kasar Sin.

Yau Litinin ne shugabannin JKS suka fara zaman taro na 3 na kwamitin kolin jam’iyyar karo na 20, inda za a tsara ayyukan da ke shafar fannin kara zurfafa yin gyare-gyare a gida daga dukkan fannoni, na zamanantar da kasar Sin.

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kasashen duniya na sa ran cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar wa duniya kyakkyawar makomar ci gaba, da kuma samar wa kamfanonin kasa da kasa sabbin damammaki. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai
Daga Birnin Sin

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya
Daga Birnin Sin

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%
Daga Birnin Sin

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Next Post
Fityanul islam

Fityanul Islam Ta Nesanta Kanta Daga Zanga-zangar Da Ake Shirin Yi

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025
An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

An Yi Taron Tattaunawa Mai Taken “Shugabancin Duniya Da Samun Wadata Tare A Yankin Asiya Da Pasifik” A Beijing

October 26, 2025
Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

Sin Da Amurka Sun Cimma Matsaya Dangane Da Tsare-Tsaren Warware Batutuwan Cinikayya Da Suke Mayar Da Hankali A Kai

October 26, 2025
Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

Sharhi: Wannan Manufar Sin Za Ta Sa Kaimin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.