Gwamnatin Tarayya ta bayar da tabbacin cewa tana kokarin shawo kan matsalar karancin abinci kuma nan ba da jimawa ba farashin kayan masarufi zai sauko.
Alkaluman baya-bayan nan daga rahoton hukumar kididdiga ta kasa (NBS), sun nuna cewa hauhawar farashi ta zarta kaso 40 cikin 100 a ‘yan watannin baya, abin da ya sanya farashin kayan masarufi ya fi karfin miliyoyin mutane.
- Sin Ta Fadada Manufar Yada Zango A Kasar Ba Tare Da Biza Ba Zuwa Karin Tashoshi
- Gdpn Sin Ya Karu Da Kashi 5% A Watanni Shida Na Farkon Bana
Sai dai karamin ninistan aikin gona, Aliyu Abdullahi, ya ce dimbin tsare-tsaren da gwamnatin tarayya ta bijiro da su, za su sassauta farashin kayan masarufin.
Ya bayyana haka ne cikin wani shiri na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
“Za a ga dimbin tsare-tsaren da aka bijiro da su domin sassauta yanayin.”
A cewar Abdullahi, “harkar noma abu ne da yake da lokaci. A halin yanzu, ana ta aikin gona. A cikin damina muke kuma idan ka kalli gonaki, za ka ga ana ta aikin noma. Shuke-shuken ba su zamo abinci ba.
“Za su zamo abinci ne kawai bayan kimanin watanni uku. Don haka, kafin wannan lokaci, haka labarin da kake nema zai ci gaba da kasancewa.”
Ministan ya ce a baya kasar nan ta dogara ne a kan noman damina.
Sai dai ya sanar da cewa ma’aikatarsa na kokarin shawo kan matsalar, inda ya ce “mun gano cewar tsawon shekaru ba ma daukar noman rani da muhimmanci.”