Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin Kebbi, ta fara saurarem karar zaben fidda-gwani na jam’iyyar PDP na mazabun kujerar dan majalisar wakilai na kananan hukumomin Argungu da Augie tsakanin Sani Yakubu da Injiniya Garba Haruna.
An shigar da karar ne a gaban kotun karkashin jagorancin mai shari’a Babagana Ashigar, wanda Sani Yakubu Augie ya shigar da Injiniya Garba Haruna, INEC da PDP domin sauya sunansa bayan ya lashe zaben fidda-gwani na mazabun Argungu/Augie a matsayin dan takarar kujerar dan majalisar tarayya mai neman tsayawa takara a zaben 2023.
- Abu Zubaydah Da Aka Yi Wa Lakabin “Dadadden Fursuna”
- An Sallami Osinbajo Daga Asibiti Bayan Yi Masa Tiyata
Lauyan wanda ya shigar da kara, J. J Usman (SAN) da wasu lauyoyi hudu, sun shaida wa kotun cewa sun gabatar da dukkan takardun karar a gaban kotu kuma an bai wa duk wadanda ake kara takardunsu.
Ya kuma ce dangane da kotu a shirye suke su ci gaba da gudanar da kararsu da hujojinsu a gaban kotun.
Har ila yau, lauyan wanda ake tuhuma na farko, Barista Hussaini Zakariya (SAN), wanda ya bayyana tare da wasu lauyoyi guda hudu, ya bayyana cewa su ma sun gabatar da dukkan takardun bayanan kariya tare da amince wa da hidimar ayyukan masu shigar da kara sannan suka bayyana shirinsu kan kare dukkan zarge-zargen da ake yi wa wanda suke kare wa,” in ji shi”.
Sai kuma mai kara na biyu da kuma lauya na uku, Barista Godwin Obibike da Barista Nura Bello sun amince da aikin da lauyan wanda ya shigar da karar ya shigar da su sannan kuma sun tabbatar wa kotu kan shigar da nasu takardun kariya.
Da yake gabatar da karar ga kotun, lauyan mai kara Barista J.J Usman (SAN), ya ce yanzu an shigo da al’amura kuma har yanzu shari’ar ta kai ga fara sauraren karar.
Sauran lauyoyin kuma sun yarda cewa a yanzu shari’ar ta balaga don fara sauraron karar da ta dace.
A nata bangaren, kotun ta ce” bayyana kammala sauraren dukkan bangarorin lauyoyin, ta bayyana cewa an dage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Agusta 2022 don ci gaba da shari’ar.”