Kungiyar Kwadago Ta Kasa reshen Jihar Kebbi (NLC), tare da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) da sauran kungiyoyi sun gudanar da zanga-zangar lumana a manyan titunan birnin Kebbi, a jihar Kebbi kan goyon bayan yajin aikin da ASUU ke yi.
Karkashin jagorancin shugaban kungiyar NLC reshen jihar Kebbi, Kwamared Umar Halidu Alhasaan, masu zanga-zangar dauke da rubuce-rubuce daban-daban, kamar “kawo karshen yajin aikin ASUU yanzu, rufe jami’o’i yana da illa ga tattalin arziki, siyasa, likitanci, al’umma da shari’a.
- Zaben Fidda-Gwanin PDP: Kotu Ta Fara Sauraren Karar Dan Majalisar Argungu/Augie a Kebbi
- NNPP Ga Buhari: Ka Sanya Dokar Ta Baci A Jihohin Arewa 5
Haka kuma ya zama damuwa ga zaman ‘ya’yanmu a gida wanda ba karamin matsala zai haifar ga yaranmu da mu kan mu iyaye.
Bisa ga hakan muna kira ga gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya sa baki domin kawo karshen yajin aikin malaman jami’o’in kasa nan .
Da yake jawabi shugaban NLC a jihar Kebbi, Kwamared Umar Halidu Alhassan ya bayyana cewa “Shugabanni kwadagon sun fito kan tituna domin gudanar da zanga-zangar domin daliban da abin ya fi shafa su ne ‘ya’yan talakawa da ke makarantun gwamnati.
“ASUU ta shiga yajin aikin watanni biyar da suka gabata, kuma mafi yawan wadanda abin ya shafa ‘ya’yan talakawa ne, abin da muke yi a yau ba wai don kawo karshen yajin aikin ba ne, sai dai fafutukar ganin an samar da ingantaccen ilimi, kuma mafi kyawun ababen more rayuwa a cikin jami’o’i, inji shugaban.
Ya kara da cewa, NLC za ta ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana har sai an magance matsalar ta yadda ya kamata, inda ya jaddada cewa, ma’aikatan ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen shiga cikin kulle-kulle baki daya.
A nasa jawabin, shugaban ASUU na jihar Kebbi, Kwamared Yayale Ibrahim Danjuma, ya ce “yajin aikin ya zama dole domin kara matsawa gwamnati lamba don ganin ta cika alkawarin da ta dauka.”
Yaa jaddada cewa, jami’o’in na da karancin kayan aikin koyar da dalibai, alhalin albashin malamai ba ya isarsu.
Hakazalika, shugaban kungiyar dalibai a jihar, Muhammed Muhaed Manjo, ya kuma bayyana cewa ilimi hakki ne na dukkan ‘ya’yan Nijeriya, ba gata ba ne, ya jaddada cewa, sun gaji da zama a gidajensu, ya kuma yaba wa ASUU, NLC da suka yi hadin gwiwa don gudanar da zanga-zangar lumana.
A sakon shugaban kungiyar NLC ta kasa, wanda ya shugaban kungiyar na jihar Kebbi ya wakilta , Kwamared Alhassa, a yayin gabatar da takardar zanga-zangar ta su ga Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, ya yaba wa gwamnan bisa kasancewa cikin gwamnoni biyar da suka biya ‘yan fansho garatuti da biyan albashin ma’aikata a kai a kai da kuma jajircewa wurin jin dadin al’umma a Jihar kebbi.
Ya bayyana cewa, sun je gidan gwamnati ne domin gabatar masa da wasikar zanga-zangar su domin ya shiga cikin maganar yajin aikin ASUU, ya jaddada cewa, a matsayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin Jam’iyyar APC da ya sa baki don kawo karshen yajin aikin da aka dade ana yi a jami’o’in kasa mu Nijeriya.
A nasa martanin, Glgwamna Abubakar Atiku Bagudu, wanda ya bayyana yajin aikin a matsayin abin damuwa, ya kuma bukaci kungiyoyin kwadago a jihar da su fito da hanyoyin da za a bi domin kawo karshen yajin aikin da kuma yadda za a samar da kudade a fannin ilimi a Nijeriya.