A jiya Talata ne asusun ba da lamuni na duniya IMF ya sake bita tare da daga hasashen bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2024 zuwa kashi 5 cikin dari, a sabon hasashensa na tattalin arzikin duniya, wanda ya kasance kashi 4.6 cikin dari a watan Afrilu.
Sabon hasashen ya bayyana cewa, an danganta bitar da farfadowar sayayya da kuma yawan fitar da kayayyaki a rubuin farko.
- Matsalar Tsaro: Ɗalibai Sun Ƙaurace Wa Ɗakunan Kwana A Lakwaja
- Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Cire Rubutun Ajami A Kudin Nijeriya
Ya ce, “A kasar Sin, farfadowar sayayya cikin gida ya haifar da kyakkyawan sakamako a rubui na farko, tare da taimakon karuwar fitar da kayayyaki na wucin gadi wanda ke da alaka da karuwar bukatu daga sassan duniya a bara.”
IMF ya daidaita hasashen ci gaban duniya a shekarar 2024 a kashi 3.2 cikin dari, tare da lura da cewa, tattalin arzikin kasuwannin Asiya ya kasance babban jigon tattalin arzikin duniya.
Cinikin duniya ya karu a farkon shekara, sakamakon yawan fitar da kayayyaki daga Asiya, musamman a bangaren fasaha, a cewar sabon hasashen tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Yahaya)