Assalamualikum masu karatu,
Barkanmu da sake haduwa da ku cikin wannan mako a shirinmu na Girki Adon Mace. Yau mun kawo muku tsarabar yadda ake miyar Agushi daga Yammachin kasar Nijeriya.
Da farko dai ga abubuwan da za ku tanada; kayan miya, irinsu tattasai, attarUgu da albasa, manja, markadadden Agushi da yankakken ganyen Ugu, maggi, Nama, Crayfish
Ga kuma Yadda ake hadawa
Da farko dai za ki wanke yankaken ganyen Ugunki da ruwa da gishiri don tsabtace ganyen daga kananan kwarin da ido ba zai iya gani ba, sai ki wanke naman ki shi ma.
Bayan kin wanke nama za ki tafasa shi cikin tukunya daban da ruwa da maggi da albasa da dai kayan kamshi da ba za a rasa ba. Cikin wata tukunyar daban za ki zuba manja da albasa ta dan soye don kashe warin manja, sai ki kawo markadadden kayan miyar ki saka ta soyu a hankali, za ki saka Crayfish dinki da maggi sai ki juya ta don kar ta kone.
Idan kin gama da dahuwarta, sai ki kawo agushinki ki zuba sai ki bar ta na dan mintina sai ki dauko ganyen Ugun ki sai ki zuba ciki da tafasshshen namanki, ki juya su gaba daya har sai kin gamsu da juyawar.
Za ki iya kawo ruwan naman da kika tafasa sai ki zuba daidai yadda kike so, sai ki bar miyar a kan wita na tsawon minti 10, sannan ki sauke, shi kenan ya kammala. Za ki iya cin miyar da tuwon Alkama, tuwon garri, tuwon doya, da tuwon semo.
A ci lafiya.