Ya danganta da irin nau’in da aka shuka, amma yana fara girma ne daga sati 6 zuwa sati 14 bayan shuka shi, kafin ya kai munzalin yi masa girbi, har ila yau; akwai kuma sauki wajen shuka shi.
Yanayin Da Latas Ya Fi Bukata:
Yanayin da Latas ya fi bukata shi ne, ma’unin yanayin da ya kai daga 45 zuwa 65 (20-22˚C).
Nomansa: Don samun dimbin riba mai yawa daga amfaninsa da aka shuka da kuma samun girbi mai yawa, ana bukatar manomi ya tabbatar yana cire Ciyawarsa; akalla sau biyu kafin a yi masa girbi.
- Matasa Za Su Amfana Da Shirin Noma Don Samun Riba
- Gwamnatin Kebbi Ta Ƙaddamar Rabon Taki Ga Manoma 48,000 Kyauta
Kare Shi Daga Harbin Kwari Da Cututtuka: Ana amfani da magungunan kashe kwari, domin ba shi kariya; wanda za a iya zuba shi tsawon sati biyu ko kuma sati biyar bayan shuka shi.
Lokacin Da Ake Yi Masa Girbi: Yana kammala girma bayan an shuka shi a kimanin wata biyu, lokacin girbin farko zai iya kai wa daga kwana 40 zuwa 60, ya danganta da irin nau’insa da aka shuka.
Ribar Da Ake Samu Da Kuma Yadda Ake Hada-hadar Kasuwancinsa A Nijeriya:
Duk kilo daya na Latas, na kai wa kimanin Naira 500 a Nijeriya, sakamakon irin bukatarsa da ake yi a fadin kasar, haka nan za a iya tallansa ta kafar yanar Gizo ko a gidajen sayar da abinci da otel-otel ko kuma a yayin wani taron biki.
Yadda Ake Fara Nomansa A Nijeriya:
Za ka iya shuka shi a bayan dakinka, haka nan kuma za ka iya shuka shi a cikin Gona, don samun riba mai yawa; musamman a yanayin noma mai kyau, sannan kuma; babu wani batun jin tsoro ga wanda yake bukatar shiga wannan fanni nomansa, inda kuma aka tabbatar da cewa, Latas na cike gurbin sauran kayan lambun da ake amfani da su a cikin abinci, musamman a Kudancin wannan kasa; kazalika, sakamakon alfanun da yake da shi; ya sa bukatarsa ke ci gaba da karuwa a kasar nan.
Shirye-shiryen Nomansa Da Kayan Da Ake Bukata:
Yana girma a kasar noman da aka gyara ta, amma bayan girma a gurin da ake samun zaizayar kasa, a farko ana shuka Irinsa don renon sa kafin a canza masa guri, wannan ya danganta da irin kwarewar da Manominsa yake da ita da kuma karfin aljihunsa.
Ban-ruwa: Latas ba ya bukatar ban-ruwa sosai, musamman wanda aka shuka da damina, ana kuma son kasar noman da aka shuka shi ta kasance babu danshi sosai, haka nan ban-ruwan ya kasance ana yin sa daga kwana uku zuwa kwana biyar.
Zuba Taki: Yana da kyau manomi ya yi amfani da takin gargajiya ko takin zamani, ana kuma so a zuba takin a kan lokaci; musamman ganin cewa, a cikin dan gajeren lokaci Latas din ke kammala girma, sannan ana bukatar takin ya kasance yana dauke da sinadarin ‘Potassium da na phosphorus’, idan kuma takin zamani ne, ana iya kara zuba shi daga sati shida zuwa sati takwas.