ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nazari A Kan Yanayin Da Latas Ya Fi Buƙata

by Abubakar Abba
1 year ago
Latas

Ya danganta da irin nau’in da aka shuka, amma yana fara girma ne daga sati 6 zuwa sati 14 bayan shuka shi, kafin ya kai munzalin yi masa girbi, har ila yau; akwai kuma sauki wajen shuka shi.

Yanayin Da Latas Ya Fi Bukata:

Yanayin da Latas ya fi bukata shi ne, ma’unin yanayin da ya kai daga 45 zuwa 65 (20-22˚C).

ADVERTISEMENT

Nomansa: Don samun dimbin riba mai yawa daga amfaninsa da aka shuka da kuma samun girbi mai yawa, ana bukatar manomi ya tabbatar yana cire Ciyawarsa; akalla sau biyu kafin a yi masa girbi.

  • Matasa Za Su Amfana Da Shirin Noma Don Samun Riba
  • Gwamnatin Kebbi Ta Ƙaddamar Rabon Taki Ga Manoma 48,000 Kyauta

Kare Shi Daga  Harbin Kwari Da Cututtuka: Ana amfani da magungunan kashe kwari, domin ba shi kariya; wanda za a iya zuba shi tsawon sati biyu ko kuma sati biyar bayan shuka shi.

LABARAI MASU NASABA

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa

Lokacin Da Ake Yi Masa Girbi: Yana kammala girma bayan an shuka shi a kimanin wata biyu, lokacin girbin farko zai iya kai wa daga kwana 40 zuwa 60,  ya danganta da irin nau’insa da aka shuka.

Ribar Da Ake Samu Da Kuma Yadda Ake Hada-hadar Kasuwancinsa A Nijeriya:

Duk kilo daya na Latas, na kai wa kimanin Naira 500 a Nijeriya, sakamakon irin bukatarsa da ake yi a fadin kasar, haka nan za a iya tallansa ta kafar yanar Gizo ko a gidajen sayar da abinci da otel-otel ko kuma a yayin wani taron biki.

Yadda Ake Fara Nomansa A Nijeriya:

Za ka iya shuka shi a bayan dakinka, haka nan kuma za ka iya shuka shi a cikin Gona, don samun riba mai yawa; musamman a yanayin noma mai kyau, sannan kuma; babu wani batun jin tsoro ga wanda yake bukatar shiga wannan fanni nomansa, inda kuma aka tabbatar da cewa, Latas na cike gurbin sauran kayan lambun da ake amfani da su a cikin abinci, musamman a Kudancin wannan kasa; kazalika, sakamakon alfanun da yake da shi; ya sa bukatarsa ke ci gaba da karuwa a kasar nan.

Shirye-shiryen Nomansa Da Kayan Da Ake Bukata:

Yana girma a kasar noman da aka gyara ta, amma bayan girma a gurin da ake samun zaizayar kasa, a farko ana shuka Irinsa don renon sa kafin a canza masa guri, wannan ya danganta da irin kwarewar da Manominsa yake da ita da kuma karfin aljihunsa.

Ban-ruwa: Latas ba ya bukatar ban-ruwa sosai, musamman wanda aka shuka da damina, ana kuma son kasar noman da aka shuka shi ta kasance babu danshi sosai, haka nan ban-ruwan ya kasance ana yin sa daga kwana uku zuwa kwana biyar.

Zuba Taki: Yana da kyau manomi ya yi amfani da takin gargajiya ko takin zamani, ana kuma so a zuba takin a kan lokaci; musamman ganin cewa, a cikin dan gajeren lokaci Latas din ke kammala girma, sannan ana bukatar takin ya kasance yana dauke da sinadarin ‘Potassium da na  phosphorus’, idan kuma takin zamani ne, ana iya kara zuba shi daga sati shida zuwa sati takwas.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani
Noma Da Kiwo

Tinubu Ya Zuba Naira Tiriliyan 1.5 Don Bunkasa Noma Da Kayan Aiki Na Zamani

November 14, 2025
Rashin Daukar Tsauraran Matakai Na Iya Durkusar Da Bangaren Noma – Shehu Galadima
Noma Da Kiwo

Dalilin Asusun NADF Na Yin Hadaka Da Gwamnatin Jihar Jigawa

November 14, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista
Noma Da Kiwo

Shirin Shugaba Tinubu Na ‘Renewed Hope’ Zai Karfafa Wa Manoma Gwiwa – Oyebanji

November 7, 2025
Next Post
Jami’an DSS Sun Cafke Waɗanda Suka Yi Garkuwa Da Mahaifiyar Rarara

Jami'an DSS Sun Cafke Waɗanda Suka Yi Garkuwa Da Mahaifiyar Rarara

LABARAI MASU NASABA

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Hallaka Dama-Dama

NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Hallaka Dama-Dama

November 15, 2025
Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

Masu Kokarin Kashe Kansu Na Kara Karuwa A Nijeriya

November 15, 2025
Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

Wakilai Daga Jihohi 19 Sun Isa Ibadan Don Taron PDP Na Ƙasa

November 15, 2025
Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

Daliban FUTA 240 Sun Samu Digiri Mai Daraja Ta Daya

November 15, 2025
Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

Shakirat Ta Tsallaka Mataki Na Ƙarshe Na Zama Gwarzuwar Ƴar Wasan Afrika

November 15, 2025
Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

Wasu Mahara Sun Kashe Mata 2, Tare Da da Ƙona Gidansu A Tudun Yola

November 15, 2025
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

Rundunar Sojin Nijeriya Ta Bayyana Dalilan Hana Jami’anta Auren ‘Yan Kasashen Waje

November 15, 2025
Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

Fashi Da Makami: An Yanke Wa ’Yan Nijeriya Hudu Mazauna Birtaniya Hukuncin Daurin Shekara 55 A Gidan Yari

November 15, 2025
Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

Shugaban APC Na Kano Ya Nemi Afuwa Daga Al’ummar Fagge Kan Kalamansa

November 15, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

’Yansanda Sun Cafke Wani Da Ake Zargin Dan Ta’adda Ne A Jihar Kebbi

November 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.