Idan kana bukatar samun riba da wuri wajen noma, ba tare da daukar dogon lokaci ba; wadannan su ne amfanin gonar da ya kamata ka shuka, musamman a lokacin damina; domin kuwa suna girma ne a cikin akalla kwana 90, wanda a cikin dan kankanin lokaci ake samun kudi.
- Kankana: Ana iya shuka Kankana a kowane bangare na kasar nan, sannan nauyinta na kai wa akalla kilo tara; haka nan ana iya yin nomanta kimanin sau uku ko hudu a shekara, kazalika; a tabbatar da ana yi mata ban-ruwa sosai tare da zuba mata taki, domin kuwa ana iya girbe kimanin tan biyu a lokaci guda.
- Kwakwamba: Za a iya samun ribar akalla Naira miliyan biyar a kadada daya cikin wata biyar bayan shuka ta, domin kuwa duk buhunta daya za a iya samun daga Naira 3000 zuwa Naira 7,000.
- Birnin Beijing Zai Kara Yawan Lambunan Shakatawa
- Dalibai 4000 Ne Suka Shiga Noman Kayan Lambu Na Zamani – Dakta Bello
Ana yin nomanta a Kudanci da kuma Arewacin Nijeriya, ya danganta da girman gonar da aka shuka ta, sannan kuma an kiyasta cewa, za a iya girbe kimanin buhu 1,500 a kowace kadada daya, ya danganta da irin nau’in da aka shuka.
- Tumatir:
Tumatir na daya daga amfanin gonar da ake amfani da shi wajen yin miya, sannan kuma yana dauke da sinadaran da suka hada da; ‘bitamins A, C’ da sauransu.
Za a iya girbe kimanin tan 90 na Tumatir a kadada daya, kazalika sama da mutane miliyan 200 ne ke amfani da Tumatir a daukacin fadin kasar nan.
Ana kuma iya samun sama da tan 60,000, wanda kudinsa ya kai sama da Naira biliyan 11.
- Kubewa: Kubewa na daya daga cikin amfanin da ake samun dimbin kudaden shiga, haka nan mutane da dama na yin amfani da ita wajen yin miya, haka nan kuma; nomanta ba shi da wata wahala, musamman ga wadanda za su noma ta domin samun riba.
Haka zalika, za ka shuka Kubewa a cikin gidanka; za kuma ta iya girma kamar yadda ake bukata, inda take kammala girmanta a cikin kwana 40.
Har ila yau kuma, idan aka shuka Irinta, za a iya samun amfani sama da dari, har ila yau kuma; za a iya sayar da Irinta don samun kudaden shiga.
- Yalon Bello:
Shi ma na daya daga cikin wadanna amfanin gona da ke girma da wuri, musamman domin bukatu biyu da suka hada da abinci da kuma sarrafa magunguna.
Har ila yau, ana cin ganyensa; haka nan ganyen ana sayar da shi ko kuma a yi amfani da shi a wajen dafa abinci, sannan kuma idan an shuka shi, yana da saurin girma.
Bugu da kari kuma, nomansa ba shi da wata wahala; sannan nau’ikansa sun hada da; fari da sauransu.
- Ugwu: Ana noma shi, musamman domin dalilai biyu da suka hada da, miya; inda kuma a Nijeriya ake sarrafa magungunan gargajiya da shi.
Bugu da kari, zai yi wuya ka ga ‘yan kabilar Igbo sun yi miya ba tare da amfani da shi ba, haka nan wasu al’ummar yankunan kudancin kasar nan da kuma Arewacin Nijeriya; su ma suna amfani da shi wajen yin miya.
Ana samun riba mai yawa a Ganyen, inda kuma ake girbinsa a cikin kwana 30, bayan shuka shi.
Har ila yau, manoma da dama a kasar nan; na nomansa har zuwa tsawon shekara, haka manomin da yake son nomansa a lokacin kakar rani, dole ne ya tabbata ya tanadi kayan ban- ruwa.
- Attaruhu:
Shi ma wannan kayan lambun, na daya daga cikin amfanin gonar da ke girma da wuri, domin kuwa ana shuka Irinsa a kan kunya ko a cikin wani sunduki ko roba, haka nan kuma yana dauke da sinadarin ‘bitamins A, B, C’, ana kuma amfani da shi wajen magance wasu cututtuka da suka hada da; ciwon sanyi da na gwiwa, cutar daji da sauransu.
Ana kuma samun dimbin kudade bayan an girbe shi, inda kuma a kadada daya, manominsa zai iya samun kimanin tan 40, ya danganta da nau’insa wanda manomin nasa ya shuka.
- Kabeji: Wannan amfanin na daya daga cikin amfanin gona da ake iya samun kudaden shiga a cikin kwana dari, haka ana iya yin nomansa a kowane yanki da ke fadin kasar nan.
Bayan shuka shi, yana kai wa daga kwana 50 zuwa 70, inda kuma wani kuma ke kai wa daga kwana 70 zuwa 90 ko kuma daga kwana 90 zuwa 125 kafin ya kammala girma, ya danganta da irin nau’insa da aka shuka.
Har ila yau kuma, a kadada daya da aka shuka shi, manomi zai iya samun tan 80, amma idan an ba shi kulawar da ya dace.
- Rama: Rama na daya daga cikin amfanin gonar da ke girma da wuri, haka nan ana shuka ta akasari a Arewacin kasar nan, kuma za a iya shuka ta a kowane yankin da ke kasar.
Haka zalika, kula da ita ba shi da wata wahala, shi yasa ake bayar da shawara a rika zuba mata takin gargajiya.
Maominta zai iya samun kuadaden shiga masu yawa, inda kuma aka kiyasat cewa, a kadada daya da aka noma ta, za a iya samun kudin shiga da su ka kai kimain naira 500,000.
- Masara: Masara na daya daga cikin jerin wadannan amfanin gona, inda ake bukatar manomin da ke sha’awar shiga fannin noman, ya tabbatar ya gyara gonar yadda ya kamata
Ana kuma bukatar a zuba taki yadda ya dace, domin ta yi saurin girma, ana kuma so a bi dukkannin ka’idojin da masana suka gindaya wajen nomanta, musamman don samun dimbin kudaden shiga.