ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kayan Lambun Da Manomi Zai Iya Girbewa A Wata Uku

by Abubakar Abba
2 years ago
Lambu

Idan kana bukatar samun riba da wuri wajen noma, ba tare da daukar dogon lokaci ba; wadannan su ne amfanin gonar da ya kamata ka shuka, musamman a lokacin damina; domin kuwa suna girma ne a cikin akalla kwana 90, wanda a cikin dan kankanin lokaci ake samun kudi.

  1. Kankana: Ana iya shuka Kankana a kowane bangare na kasar nan, sannan nauyinta na kai wa akalla kilo tara; haka nan ana iya yin nomanta kimanin sau uku ko hudu a shekara, kazalika; a tabbatar da ana yi mata ban-ruwa sosai tare da zuba mata taki, domin kuwa ana iya girbe kimanin tan biyu a lokaci guda.
  2. Kwakwamba: Za a iya samun ribar akalla Naira miliyan biyar a kadada daya cikin wata biyar bayan shuka ta, domin kuwa duk buhunta daya za a iya samun daga Naira 3000 zuwa Naira 7,000.
  • Birnin Beijing Zai Kara Yawan Lambunan Shakatawa
  • Dalibai 4000 Ne Suka Shiga Noman Kayan Lambu Na Zamani – Dakta Bello

Ana yin nomanta a Kudanci da kuma Arewacin Nijeriya, ya danganta da girman gonar da aka shuka ta, sannan kuma an kiyasta cewa, za a iya girbe kimanin buhu 1,500 a kowace kadada daya, ya danganta da irin nau’in da aka shuka.

  1. Tumatir:

Tumatir na daya daga amfanin gonar da ake amfani da shi wajen yin miya, sannan kuma yana dauke da sinadaran da suka hada da; ‘bitamins A, C’  da sauransu.

ADVERTISEMENT

Za a iya girbe kimanin tan 90 na Tumatir a kadada daya, kazalika sama da mutane miliyan 200 ne ke amfani da Tumatir a daukacin fadin kasar nan.

Ana kuma iya samun sama da tan 60,000,  wanda kudinsa ya kai sama da Naira biliyan 11.

LABARAI MASU NASABA

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu

  1. Kubewa: Kubewa na daya daga cikin amfanin da ake samun dimbin kudaden shiga, haka nan mutane da dama na yin amfani da ita wajen yin miya, haka nan kuma; nomanta ba shi da wata wahala, musamman ga wadanda za su noma ta domin samun riba.

Haka zalika, za ka shuka Kubewa a cikin gidanka; za kuma ta iya girma kamar yadda ake bukata, inda take kammala girmanta a cikin kwana 40.

Har ila yau kuma, idan aka shuka Irinta, za a iya samun amfani sama da dari, har ila yau kuma; za a iya sayar da Irinta don samun  kudaden shiga.

  1. Yalon Bello:

Shi ma na daya daga cikin wadanna amfanin gona da ke girma da wuri, musamman domin bukatu biyu da suka hada da abinci da kuma sarrafa magunguna.

Har ila yau, ana cin ganyensa; haka nan ganyen ana sayar da shi ko kuma a yi amfani da shi a wajen dafa abinci, sannan kuma idan an shuka shi, yana da saurin girma.

Bugu da kari kuma, nomansa ba shi da wata wahala; sannan nau’ikansa sun hada da; fari da sauransu.

  1. Ugwu: Ana noma shi, musamman domin dalilai biyu da suka hada da, miya; inda kuma a Nijeriya ake sarrafa magungunan gargajiya da shi.

Bugu da kari, zai yi wuya ka ga ‘yan kabilar Igbo sun yi miya ba tare da amfani da shi ba, haka nan wasu al’ummar yankunan kudancin kasar nan da kuma Arewacin Nijeriya; su ma suna amfani da shi wajen yin miya.

Ana samun riba mai yawa a Ganyen, inda kuma ake girbinsa a cikin kwana 30, bayan shuka shi.

Har ila yau, manoma da dama a kasar nan; na nomansa har zuwa tsawon shekara, haka manomin da yake son nomansa a lokacin kakar rani, dole ne ya tabbata ya tanadi kayan ban- ruwa.

  1. Attaruhu:

Shi ma wannan kayan lambun, na daya daga cikin amfanin gonar da ke girma da wuri, domin kuwa ana shuka Irinsa a kan kunya ko a cikin wani sunduki ko roba, haka nan kuma yana dauke da sinadarin ‘bitamins A, B, C’, ana kuma amfani da shi wajen magance wasu cututtuka da suka hada da; ciwon sanyi da na gwiwa, cutar daji da sauransu.

Ana kuma samun dimbin kudade bayan an girbe shi, inda kuma a kadada daya, manominsa zai iya samun kimanin tan 40, ya danganta da  nau’insa wanda manomin nasa ya shuka.

  1. Kabeji: Wannan amfanin na daya daga cikin amfanin gona da ake iya samun kudaden shiga a cikin kwana dari, haka ana iya yin nomansa a kowane yanki da ke fadin kasar nan.

Bayan shuka shi, yana kai wa daga kwana 50 zuwa 70, inda kuma wani kuma ke kai wa daga kwana 70 zuwa 90 ko kuma daga kwana 90 zuwa 125 kafin ya kammala girma, ya danganta da irin nau’insa da aka shuka.

Har ila yau kuma, a kadada daya da aka shuka shi, manomi zai iya samun tan 80, amma idan an ba shi kulawar da ya dace.

  1. Rama: Rama na daya daga cikin amfanin gonar da ke girma da wuri, haka nan ana shuka ta akasari a Arewacin kasar nan, kuma za a iya shuka ta a kowane yankin da ke kasar.

Haka zalika, kula da ita ba shi da wata wahala, shi yasa ake bayar da shawara a rika zuba mata takin gargajiya.

Maominta zai iya samun kuadaden shiga masu yawa, inda kuma aka kiyasat cewa, a kadada daya da aka noma ta, za a iya samun kudin shiga da su ka kai kimain naira 500,000.

  1. Masara: Masara na daya daga cikin jerin wadannan amfanin gona, inda ake bukatar manomin da ke sha’awar shiga fannin noman, ya tabbatar ya gyara gonar yadda ya kamata

Ana kuma bukatar a zuba taki yadda ya dace, domin ta yi saurin girma, ana kuma so a bi dukkannin ka’idojin da masana suka  gindaya wajen nomanta, musamman don samun dimbin kudaden shiga.

Lambu
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari A Kan Wasu Cututtuka Da Ke Shafar Dabbobi Lokacin Damina
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    “Mutunta Ƴancin Addinai Ita Ce Hanyar Wanzar Da Zaman Lafiya A Kaduna”

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Noma Da Kiwo

Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa

July 11, 2026
Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu
Noma Da Kiwo

Me Ya Sa Har Yanzu Manoma A Arewa Suka Gwammace Yin Noma Da Galmar Shanu

July 4, 2026
Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana
Noma Da Kiwo

Dalilin Masu Kiwon Kajin Gidan Gona Na Sukar Haɗakar Gwamnatin Tarayya Da Chana

July 3, 2026
Next Post
Batun Biyan Dubu ₦105 Mafi Ƙarancin Albashi Ƙanzon Kurege Ne – Fadar Shugaban Ƙasa

Tsoratar Da Mu Aka Yi Da Ƙara Kuɗin Fetur, Muka Amince Da Mafi Ƙarancin Albashi Na Dubu ₦70 - Ƴan Ƙwadago

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.