Akalla mutane 36 ne wasu ‘yan bindiga da suka kai wa al’ummar yankin Keke B da ke cikin garin New Millennium a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna suka yi garkuwa da su a ranar Litinin da daddare.
An kai harin ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Litinin, yayin da mazauna yankin da dama ba su dawo daga aiki ba.
- An Bude Taron Dandalin Kare Hakkin Dan Adam Na Beijing Na Shekarar 2022
- Goje Ya Raba Taki Na Naira Miliyan 300 Ga Manoman Gombe
Duk da cewa jami’an rundunar ‘yan sanda ta ce tana kokarin tantance adadin mutanen da aka sace, wani mazaunin garin ya shaida wa wakilinmu cewa an yi garkuwa da mutane kusan 36.
Wani mazaunin garin wanda ya tabbatar da faruwar harin, ya shaida wa LEADERSHIP cewa, “Masu garkuwar sun zo ne da misalin karfe 9:00 na dare a lokacin da ake ruwan sama. Sun yi garkuwa da mutane kusan 36. Galibin mutanen da aka yi garkuwa da su suna kan hanyar komawa gida ne kawai suka yi kacibu da ‘yan bindigar.
Wani shaidan gani da ido ya ce ‘yan bindigar sun rika kai farmaki gida-gida ba tare da kakkautawa ba.
A cewar wani mazaunin garin, Muhammad Salihu, “Da yawa daga cikinmu muna waje lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari saboda da karfe 9 na dare ne. Sun zo da yawansu, suka dinfa harbi ta ko ina.
“Sun shiga gidajen mutane daya bayan daya suka yi garkuwa da mutanen. Mutum daya mai bakaniken babur ne ya iya tserewa daga hannunsu, amma sun tafi tare da mutane 36.”
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, an kasa samun damar jin ta bakinsa saboda wayarsa ba ta shiga.