Kwalejin ilimi ba su yin abinda ya dace saboda ba a basu wani muhimmancin da ya kamata ba, hakan ma shi yasa lamarin koyarwa ya kasance wuri na karshe na wadanda suka kammala jami’a ba su kuma sha’awar aikin koyarwa,ba su kuma a shirya su koyi yadda za su koyar yadda ya dace.Domin kuwa suna yin aikin koyarwa ne kawai domin su samu hanyar biyan bukatunsu.
Shi ya sa masu makarantu ba shirye suke ba su rika basu albashin da ya dace ba,saboda yadda suka dauki malaman makaranta ba da wata daraja ba.Haka lamarin yake sai dai kuma ba a taru aka zama daya ba.
- Sufeton ‘Yansanda Ya Amince Da Zanga-zangar Matsin Rayuwa, Ya Gindaya Sharadi
- Muhimmin Sakon Kwankwaso Ga ‘Yan Nijeriya Kan Shirin Zanga-zanga
Alalade ya kara yin bayani inda yake cewa rashin isassun malaman makaranta abin ba ya tsaya kadai bane kan Lissafi da Turanci,a takaice dukkan darussan.“Daga cikin ‘ya’yanmu namu muke son su zama malaman makaranta? Iyaye nawa suke fatan ‘ya’yansu su zama malaman makaranta? Makarantu nawa ko manyan makarantu suke koyarwa da manufar jan hankalin ‘yan makarantar su yi sha’awar aikin koyarwa?
Abin so ne a a daukaka darajar malaman makaranta ta kasance irin ta ma’aikatan Banki ko kuma masu aiki a kamfanin mai,domin yin hakan zai iya sa abubuwa a canza yadda ake Kallon malaman makaranta, daga haka kuma za a fara ganin sauyi daga yadda suke gudanar da aikinsu.Muna sa ‘ya’yanmu amakaranta ne domin su yi aikin da bai danganta da koyarwa, idan kuma ba mu yi haka ba maganar karancin malamai a darussan Lissafi da Turanci abin zai kara kazancewa ne.Lukaci ya yi wanda dole ne sai mun canzawa matasa yadda ya dace da kamata su kaunaci aikin koyarwa da su malaman makaranta.
Kamata ya yi a fara yanzu domina sauya tunanin wasu dalibai su rungumi aikin koyarwa saboda a gaba a samu wadanda za su yi aikin bilhakki da gaskiya.Dole ne a samo mafita na tsaro da wasu manufofin da sharuddan da za su jan hankalin wadanda basu sha’wara yin aikin malamain makaranta su yi sha’awar haka.Sai dai tambayar ita ce wanene, ko kuma me zai koyawa ‘ya’yanmu da jikokinmu idan ba a yi tsarin da abin zai jawo hakali ba, ai zai wuyar ka tallata abinda ba ka tanada ba!”
Iyaye da basu son ‘ya’yansu su zama malaman makaranta
“Akwai abin da ke bada gudunmawa wajen rashin isassun malaman da za su koyar a darussan Turanci da Lissafi. Abin mamaki shi ne iyaye na bukatar a koya wa ‘ya’yansu amma basu bukatar ‘ya’yansu su zama malaman makaranta.Ko wa ai ya san dalilin domin kuwa iyaye sun bar maida hankali a kan irin kokarin da ‘ya’yansu suke yi kamar yadda ya dace tun da farko su yi hakan.Ba su damu ba koma wanene zai koyawa ‘ya’yansu, su kawai abin da suke bukata ‘ya’yan su kasance sun samu zuwa ajin SS2.
Daga nan kuma sai ta wacce hanya ‘ya’yan nasu za su rubuta jarabawa sanin kowa ne kuma irin haka ne har sai aki ga bata lokaci saboda lokaci ya kure.Ya dace iyaye su maida hankali kamar yadda ya dace dangane da lamarin ilimin ‘ya’yansu.Su bada duk wata gudunmawar da suka za ta taimaka wajen ilimin da ‘ya’yansu za su samu mai nagarta,matukar idan har basu bukatar a rika ba ‘ya’yansu duk abin da aka ga dama da suna albashi,idan ba fata da bukatar kaiwa ga haka, a kula da malaman makaranta wajen biyansu albashi mafi tsoka ta haka ne ‘ya’yanku da jikokinsu za su samu ilimi mai inganci.”