Tsohon na hannun daman shugaba Muhammadu Buhari, Buba Galadima, ya bayyana cewar bisa halin rashin tsaro da yaki ci yaki cinyewa a kasar nan, ba zai zama wani abun mamaki ba idan har aka yi garkuwa da shugaban kasar shi da kansa sukutum.
Jaridar Daily Trust ta nakalto cewa Buba Galadima na fadin hakan ne a hirarsa da BBC Hausa, inda yake koka kan halin rashin tsaro da ake ciki a kasar nan.
- Shin Zargin Kasar Sin Ya Fi Yaki Da Ta’Addanci Muhimmanci?
- Jami’an KAROTA Sun Damke Bakin Haure Dauke Da Muggan Makamai A Kano
Ya ce, “Wadannan ‘yan bindigar sun kunyata gwamnatin Buhari. A farkon gwamnatin kowa na tsoronsa (Buhari); da tsammanin cewa shi din jarumi ne amma yanzu kowa ya gane rashin kokarinsa.
“Buhari bai san komai ba, ba kuma zai iya yin komai ba, shi ya sa kuke ganin jami’an gwamnati na wakaci tashi da biliyoyin dukiyar al’umma babu kuma wanda zai iya hana su.”
Galadima ya kara da cewa, muddin har ‘yan ta’adda suka iya samun nasarar balle gidan yarin Kuje, to har shi kansa ‘Buhari’ ma bai tsira ba.
Ya kara da cewa, “Idan ba a dauki matakin ba, yanzu ko nan gaba masu garkuwar nan za su iya sace Buhari bisa lura da yadda ake nuna halin ko in kula da lamarin tsaro.
“Kawai yanzu mafitar da ya rage mana ita ce ko mu ci gaba da addu’a ko mu kare kanmu, amma in muka ci gaba da tunanin wannan gwamnatin ce za ta kare mu, tabbas za a kashe mu.”