Wata tawagar manyan jami’an gwamnatin Turkiyya karkashin jagorancin Ministan Harkokin Wajen Kasar, Hakan Fidan ta iya Jamhuriyar Nijar gabanin taron tattaunawar bunkasa tattalin arziki da hadakar aikin soji.
Tawagar ta kunshi ministocin tsaro da makamashi da albarkatun kasa da kuma shugaban hukumar leken asirin Turkiyya.
Wata kafar yada labarai mai zaman kanta, ActuNiger wadda ta fitar da labarin ta ce wannan ne karon farko da manyan jami’an Turkiyya ke ziyartar Nijar tun bayan da sojoji suka kwace mulkin kasar a cikin watan Yulin bara.
- An Gudanar Da Bikin Nune-Nunen Shirye-Shiryen CMG Masu Inganci A Kazakhstan Da Tajikistan
- Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Tajikistan Zai Haifar Da Sabuwar Makoma
ActuNiger ta ruwaito cewa ziyarar ta jami’an Turkiyya bibiya ce game da wata irin ta da firaiministan Nijar, Ali Lamine Zeine ya kai birnin Ankara a farkon wannan shekarar.
Turkiyya ta kasance jigo wajen hadakar aikin soji da kasashen yankin Sahel kuma wannan alaka ta kai shekara 10 tana gudana.
Kasashen biyu sun kuma kulla yarjejeniyar cinikin makamai da sauran kayan aikin soji, inda Turkiyya za ta bai wa Nijar jirgin yaki maras matuki kirar Byraktar TB2 da kuma sauran makamai da hambararren shugaban kasar Mohammed Bazoum ya saya.