Shugaba Bola Tinubu ya isa filin jirgin sama na Kotoka da ke birnin Accra na kasar Ghana a ranar Asabar.
Ya isa kasar ne don taron hadin gwiwar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) karo na shida, wanda zai fara a ranar Lahadi.
- Sin Tana Kara Yin Kwaskwarima A Dukkan Fannoni Don Samar Da Sabuwar Dama Ga Duniya
- Tsoratar Da Mu Aka Yi Da Ƙara Kuɗin Fetur, Muka Amince Da Mafi Ƙarancin Albashi Na Dubu ₦70 – Ƴan Ƙwadago
Wata kungiyar jami’an Nijeriya da suka hada da ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Tuggar, da kuma Jakadan Nijeiriya a Ghana, Ambasada Dayo Adeoye, ne suka tarbi shugaba Tinubu.
A matsayinsa na shugaban kungiyar ECOWAS, shugaba Tinubu zai yi magana game da hadewar yankin a Afirka, inda zai mayar da hankali kan nasarori da kalubale a yammacin Afirka tun bayan taron karshe a birnin Nairobi na kasar Kenya, a watan Yulin 2023.
Zai kuma gabatar da rahoton “2024 a kan yanayin al’umma,” wanda ya shafi batutuwa kamar zaman lafiya, tsaro, mulki da ci gaban zamantakewa.
Taron zai mayar da hankali ne kan taken AU na 2024: “Ilimi da fasaha a Afirka na karni na 21.”
Leadership ta ruwaito shugaba Tinubu ya bar Abuja zuwa taron kungiyar AU da safiyar ranar Asabar.