Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya kare Aliko Dangote, inda ya bayyana cewa ba a kamata a zargi Dangote da sayen daloli a farashi mai rahusa lokacin da yake gina matatar mai ba.
Sarkin ya bayyana cewa Babban Bankin Nijeriya (CBN) ne, ya samya farashin canjin kudi ga kowa a wancan lokacin, don haka ba Dangote ne ya bayar da shawarar sayar da dalar a haka ba.
- Babban Dalilin Sake Neman Ƙarin Naira Tiriliyan 6.2 Kan Kasafin Kuɗin 2024 – Bagudu
- ASUU Reshen Jami’ar Abuja Ta Janye Yajin Aiki Bayan Shafe Kwana 82
Ya jaddada cewa abin da Dangote ya yi, ya yi daidai da farashin da CBN ta yanke kuma ba daidai ba ne a kebance shi don sukarsa a kan lamarin ba.
Sanusi, ya kuma bayyana cewa fifita canjin kudin kasashen waje ga babban aiki kamar matatar mai ta Dangote abu ne da ya dace saboda tasirin da zai iya yi ga tattalin arzikin kasar.
Ya soki Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) kan gazawarsa duk da samun kudade masu yawa don gyaran matatun mai da ake da su a kasar nan.
Sanusi ya yi ikirarin cewa dogaro da samar da mai a gida ya fi aminci fiye da shigo da shigo da shi daga waje kamar yadda NNPC ke yi.
Bugu da kari, Sanusi ya karfafa wa Dangote baya, inda ya jaddada bukatar samu karin ‘yan kasuwa masu kishi a Nijeriya.
Ya yi gargadi kan cewar son kai ne ke haifar da koma baya ga masu bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasa.
Sanusi ya kuma yi kira da a yi tattauna kan ikirarin Dangote ya yi cewar akwai masu yi masa yankan-baya game da samar da man fetur a matatarsa.