ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

ASUU Reshen Jami’ar Abuja Ta Janye Yajin Aiki Bayan Shafe Kwana 82

by Abubakar Sulaiman
2 years ago
ASUU

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) reshen Jami’ar Abuja (UniAbuja) sun janye yajin aikin su na kwanaki 82 nan take. Wannan matakin ya biyo bayan tattaunawa  da sabon kwamitin gudanarwa na Jami’ar, wanda ya yi alƙawarin magance buƙatun ƙungiyar. Shugaban ƙungiyar, Dr. Sylvanus Ugoh, ya sanar da dakatar da yajin aikin bayan taron majalisar da aka gudanar a Abuja yau Litinin.

Yajin aikin ya fara ne tun a ranar 2 ga Mayu, 2024, don yin zanga-zangar nuna rashin amincewa da wasu matsaloli, ciki har da take dokokin ɗaukar ma’aikata da ƙarin girma, da kuma talla ba bisa ƙa’ida ba don neman muƙamin Shugaban Jami’ar daga gwamnatin da ta gabata.

  • Yadda Aka Kaddamar Da Kungiyar Tafiyar Matasa A Abuja
  • Har Yanzu A Gidan Haya Nake Zaune A Abuja – Aliko Dangote

Sai dai, sabon kwamitin ya yi alƙawarin soke wannan talla mai cike da cece-kuce kuma ya sake buga shi bisa ƙa’ida. Haka kuma sun amince su sake duba tsarin ɗaukar ma’aikata da ƙarin girma, musamman waɗanda aka yi a shekarar 2022/2023, da kuma gudanar da zaɓe don muƙaman Shugabannin Kwalejoji na jami’ar.

ADVERTISEMENT

Dr. Ugoh ya bayyana cewa, ƙoƙarin da aka yi a baya don warware matsalolin tare da tsohon Shugaban Jami’ar ya ci tura, wanda ya sa aka shiga yajin aikin ba tare da ƙayyadadden lokacin dawo wa ba. Amma, sabbin matakan da aka samu daga sabon kwamitin suna da kyau, wanda ya sa ƙungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin.

Kwamitin ya amince da sake duba dukkan batutuwan da suka shafi bangarorin, kuma ƙungiyar ta bayyana fatan cewa hukumar Jami’ar za ta magance matsalolin su yadda ya kamata.

LABARAI MASU NASABA

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

ASUU
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote
  • Abubakar Sulaiman
    Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa

MASU ALAKA

ASUU
Ilimi

An Tantance Masu Neman Aikin Koyarwa 500 A Jigawa

August 31, 2026
ASUU
Ilimi

JAMB Ta Ƙara Wa’adin Amincewar Guraben Karatu Zuwa 30 Satumba

August 29, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Ilimi

Kano Ta Yi Zarra Wajen Kashe Kuɗi Don Raya Ilimi A Yammacin Afirka

July 11, 2026
Next Post
Sin Ta Fitar Takardar Aiki Kan Shirin Kar A Zama Na Farkon Yin Amfani Da Makaman Nukiliya A Kan Juna

Sin Ta Fitar Takardar Aiki Kan Shirin Kar A Zama Na Farkon Yin Amfani Da Makaman Nukiliya A Kan Juna

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

Gwamnatin Tarayya Ta Gwangwaje Tawagar Kwallon Kwando Ta Mata Da Dala 100,000 Kowace

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

Sin Da Amurka Na Gudanar Da Tattaunawa Dangane Da Yiwuwar Rage Harajin Ramuwar Gayya Wanda Darajarsa Ka Iya Kaiwa Dala Biliyan 30

September 10, 2026
Gwamnatin Tarayya Ta Dakatar da Shirin Ƙara Kuɗin Jarabawar WAEC da NECO

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rika Bai Wa Ɗalibai 100MB Na Data Kyauta Kullum

September 10, 2026
Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

Sin Da Amurka Na Wanzar Da Mu’amala Game Da Shirin Ganawar Da Manyan Shugabannin Kasashen Biyu Za Su Yi A Bana

September 10, 2026
Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

Sojoji Sun Ceto Fasinjoji Uku Da ‘Yan Bindiga Suka Harba A Filato

September 10, 2026
Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

Xi Zai Halarci Taron BRICS Karo Na 18 A Indiya

September 10, 2026
Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

Rodri Ya Nemi Afuwar Valencia Dangane Da Kalaman Da Yayi Akanta

September 10, 2026
Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

Za A Gudanar Da Taron Koli Na Shugabannin Harkokin Masana’antu Da Cinikayya Na APEC Na 2026 A Shenzhen

September 10, 2026
Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

Amurka Ta Bai Wa Nijeriya Sabbin Kayan Yaƙi Domin Yaƙi Da Ta’addanci

September 10, 2026
Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.