Shugaba Bola Tinubu, ya aike wa Majalisar Dokoki kudirin dokar mafi karancin albashi domin amincewa da shi a matsayin doka.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne, shugaban kasa da shugabannin kungiyar kwadago suka amince da Naira 70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikatan Nijeriya.
- An Kama Mutane 2 Da Laifin Kashe Wani Mutum Kan ‘Maita’ A Adamawa
- An Yi Karin Haske Game Da Batutuwan Dake Shafar Sashin Tudun Ruwa Na Ren’ai
Wannan ya biyo bayan tattaunawa da shugabannin kungiyar kwadago da shugaban kasa suka yi a makonnin da suka gabata bayan watannin da suka shafe ana kai ruwa rana kan sabon tsarin mafi karancin albashin.
Kwamitin da gwamnatin tarayya ta samar, wanda ya kunshi wakilan gwamnatocin jihohi da na tarayya da masu zaman kansu, sun ba da shawarar amincewa da Naira 62,000 yayin da kungiyoyin kwadago suka dage kan Naira 250,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.
Kungiyoyin sun ce Naira 30,000 ba za ta rike ma’aikaci ba duba da yadda hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa, ke kara kamari biyo bayan cire tallafin man fetur da shugaban kasa ya yi.
Shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), Joe Ajaero, ya ce kungiyar ta amince da Naira 70,000 kuma ta yi watsi da bukatar da shugaba Tinubu ya yi na biyan Naira 250,000 a matsayin mafi karancin albashi tare da sharadin kara farashin man fetur.
Idan ba a manta, a ranar Dimokuradiyya ta 2024, Tinubu ya bayyana cewa zai aike da kudurin doka kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata ga majalisar dokokin kasar domin tantancewa.