Gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar Katsina sun kafu matuka saboda karuwar hare-haren ‘yan bindiga a wasu garuruwa da ke nuna halin ko in kula da gwamnatin ke yi wa harkar tsaro.
Wanda har yanzu ta kasa kawo karshen kisan da ake yi wa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
- Ya Kamata ‘Yan Nijeriya Su Yi Hattara Da Atiku – Magoya Bayan Tinubu
- Gwamnatin Kaduna Ta Ba Da Hutun Kwana 3 Don Jama’a Su Yi Rijistar Katin Zabe
Bayanan hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar Katsina, Abdulrahaman Abdullahi Dutsima, ya sanya wa hannu ya kuma raba wa manema labarai a Katsina.
Sanarwar ta ce ayyukan ‘yan ta’adda sun kai wani mataki da kullum sai an kai harin wuce gona da iri, saboda yadda ‘yan bindigar ke sayen makaman kare dangi da kudaden da ake biyansu, bayan sun dauke jama’a, sannan hakan na kara masu karfi ta yadda suke kara fadada kai hare-haren ba ji ba gani.
“Jihar Katsina a yau ta koma wani wuri na rashin tabbas a rayuwa babu waje buya kuma babu wanda ya tsira, hatta kokuwar Katsina tana fuskantar barazana, inda sha’anin samar da tsaron dukiya da rayukan al’umma ya zama abu na farko da shuwagabanni ya kamata su yi kafin wani abu, amma abin takaici babu wata hubbasa daga bangaren gwamnati na tunkarar wannan matsala.
Haka kuma sanarwa ta kara da cewa yanzu babu abin da ya rage sai a koma ga Allah ta hanyar yin addu’o’in neman gafarar Allah tunda duk kira da jan hankali da rubuce-rubucen an riga an yi domin jan hankalin gwamanti a kan matsalar tsaro amma shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu, zabin da rage shi ne addu’o’i.
Abdullahi, ya ce a matsayinsu na ‘yan Adam mun san cewa mulki na Allah ne kuma shi kadai ne zai yi maganin wannan matsala fiye da tunani.
Ya ce za a ci gaba da yin wadannan addu’o’i ne a masallatai da kuma majami’u da makarantun islamiyya da na allo a duk fadin jihar Katsina.
Daga karshe gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar Katsina na mika sakon ta’aziyarsu da jaje ga ‘yan uwan wadanda suka rasa ransu a sakamakon ayyukan ‘yan bindiga.
Sannan sun yin addu’ar Allah ya kawo karshen wannan mummunan yanayi da al’umma ta tsinci kanta a ciki, ya maido mata da zaman lafiya a jihar Katsina da kasa baki daya.