Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana ranakun 27, 28 da 29 ga watan Yulin 2022 a matsayin ranakun hutu domin bai wa ma’aikata a jihar cikakken damar kammala rijistan katin zabe.
Wannan bayanin na kunshe ne ta cikin sanarwar da babban mai bai wa Gwamna Nasir el-Rufai shawara a fannin yada labarai, Muyiwa Adekeye tare da rabar wa ‘yan jarida a ranar Talata.
- ‘Yan Bindiga Sun Sake Garkuwa Da Matar Shugaban Fulani A Abuja
- Rashin Tsaro: Haramta Acaba ‘Yan Nijeriya Miliyan 40 Za Su Rasa Aikin Yi – ACOMORAN
Sanarwar ta ce, “Gwamnatin jihar Kaduna ta nemi al’ummar jihar da su yi rijistar katin zabe kafin ranar rufe aikin ya zo.
“Gwamnati na kira ga dukkanin wadanda suka kai mallakar katin zaben da su yi amfani da wannan damar wajen yin rijistar domin samun damarsu ta jefa kuri’a,” cewar Adekeye.
Kazalika, gwamnatin jihar ta nemi manyan ma’aikatau da su karfafi ma’aikatansu da su yi rijistar kafin INEC ta rufe aikin rijistan.