Dakarun Sojin Operation Hadin Kai da ke yaki da mayakan Boko Haram, sun sanar da gano wata daga cikin ‘yan matan Chibok da aka sace a watan Afrilun 2014, mai suna Ihyi Abdu.
Kwamandan rundunar da ke Maiduguri, Manjo Janar Waidi Shuaibu ne, ya bayyana hakan lokacin da yake mika wadda aka gano da ‘ya’yanta guda biyu ga hukumomi a Jihar Borno.
- Da’awar Zanga-zanga: An Sako Abusalma Daga Gidan Yari
- Yarjejeniyar Beijing: Mabudin Zaman Lafiya A Zirin Gaza
Ya bayyana cewar Ihyi ta fito ne daga kauyen Kubur-Mbula da ke karamar hukumar Chibok, kuma bayan kama ta an aurar da ita ga wani da ake kira Abu Darda wanda dan assalin Jihar Filato ne amma mazaunin Gwoza kafin ya yi kaura zuwa kasar Senegal.
Kwamandan ya ce likita ya duba lafiyar Ihyi da yaranta guda biyu kuma an tabbatar suna cikin koshin lafiya.
Rundunar sojin ta kuma mika wa gwamnatin Borno wasu mutane 330 da suka hada da mata da kananan yara da dakarunta suka kubutar daga hannun Boko Haram.