Gwamnatin jihar Bauchi ta ce, babu batun wata zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar balle zancen rufe asibitoci a fadin jihar.
Sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Barista Muhammad Ibrahim Kashim ne ya sanar da matsayar gwamnati a yayin da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Laraba.
- Sakataren Gwamnati Da Ministoci Na Ganawar Sirri Kan Zanga-zangar Matsin Rayuwa
- Shugaba Tinubu Ya Bukaci ‘yan Nijeriya Da Su Soke Zanga-Zangar Da Suka Shirya
Idan za a tuna, wani jami’in gwamnatin jihar a jiya (Talata) ya shelanta cewa, su na da wani bayanin da ke cewa, akwai shirin kai hari ga asibitoci a ranar gudanar da zanga-zanga kan matsin rayuwa da ake ciki, don haka gwamnatin ta dauki matakin cewa za ta kulle dukkanin kananan asibitoci (PHCs) da suke fadin jihar a ranar zanga-zangar.
Sai dai a martaninsa, sakataren gwamnatin, ya ce wannan jami’in ya yi gaban kansa wajen sanar da batun rufe asibitoci kuma za a hukuntasa daidai da abun da ya yi.
Kan hakan, Ibrahim Kashim ya gargadi duk wani ko wasu da ke shirin gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa da cewa, ya tafi wata jiha dai ba Baachi ba, don haka ba batun zanga-zanga a jihar.
Ya ce: “Na tabbatar ku na da rahotonnin da ke zagawa cikin jihar nan da ma kasa cewa, gwamnatin jihar Bauchi ta ba da dama a rufe asibitocinta a cikin jihar da kananan hukumomi saboda zanga-zangar da ake shirin yi.
“Na daya dai, jihar Bauchi ba mu yarda da zanga-zangar nan ba kuma ba za a yi ba. Wanda ya ke da niyyar yin zanga-zanga sai dai ya je ya yi a wani waje ba dai Bauchi ba, mu Bauchi an sanmu da zaman lafiya. Kuma mu a gwamnatance mun dauki kudurin cewa za a cigaba da zaman lafiya.
“Game da maganar rufe asibitoci, shi din ma ba za a yi ba. Wanda ya ba da wannan labarin ya fada ne kawai albarkacin bakin sa kuma za a hukuntashi kamar yadda doka ta tanada.”