Bisa dukkan alamu batun gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da gamayyar kungiyoyin matasa a Nijeriya ke shirin gudanarwa na shirin shiriricewa.
Tun a farko dai, Kungiyar Matasan Arewa (Northern Nigeria Youth Forum), ita ce ta fara shelanta gudanar da wannan zanga-zanga; amma sai ga shi kuma daga bisani ta bayyana jingine shirin zanga-zangar baki daya.
Furucin Shugaban Kungiyar Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa, Kwamared Murtala Mohammed Gamji; ya yi matukar sanya shakku tare da rashin kwarin gwiwa ga daukacin matasa masu yunkurin shiga wannan zanga-zanga.
A wani taron manema labarai da ya yi, wanda LEADERSHIP Hausa ta samu kwafi, Gamji ya bayyana dalilansu na jingine wannan zanga-zanga da suka lashi takobin yi.
- Wasu Ɓata-gari Na Iya Amfani Da Zanga-zanga Domin Tada Zaune Tsaye – Minista
- Zanga-zanga-zanga: Kebbi Ta Bukaci Matasa Da Su Guji Tashe-tashen Hankula
Kwamared ya kara da cewa, sun dauki wannan matakin ne biyo bayan yadda suka gano wasu bata gari; na kokarin shirya wani mummunan makirci, ta hanyar fakewa da zanga-zangar; domin samun damar rikita kasar baki daya.
“Ni na fara shirya wannan zanga-zanga, sannan wasu mutane sun gayyace ni mun kuma zauna da su, har ma suka shaida min cewa; so suke yi a yi zanga-zangar a iya Jihohin Kaduna, Jos da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, saboda haka. Wannan dalili ne ya tilasta mana janye shirin namu, tunda tuni wasu sun fara yunkurin cimma burinsu ta hanyar yin amfani da mu”, in ji Gamji.
A karshe, Mohammed ya jaddada cewa; suna barranta kansu da masu zagin malamai da kuma masu yunkurin fakewa da wannan zanga-zanga, wajen aniyar lalata dukiyar al’umma da kuma kona kayan gwamnati; wanda ko shakka babu, babu abin da zai haifar; illa karin jawo wasu matsaloli a fadin wannan kasa tamu.
Har ila yau, a Jihar Kaduna alamu sun nuna cewa; shirin zanga-zangar babu wata makawa ya shiririce, biyo bayan rashin samun kwarin gwiwa daga manyan kungiyoyin matasan Arewa da ke jihar.
Sannan, ita Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa; tuni ta yi hannun riga tare da yin Allah wadai da shirin zanga-zangar, inda ta bukaci daukacin matasan jihar da su kaucewa shiga cikin dukkannin wata zanga-zanga da sunan tsadar rayuwa.
A zantawarsa da wakilinmun, babban mai taimaka wa Gwamnan Jihar Kaduna a kan kungiyoyin siyasa; Malam Mustapha Yamusa Rigasa, ya jawo hankalin dukkanin kungiyoyin siyasa da ke tare da gwamnatin jihar, wajen ganin sun kaurace wa shiga zanga-zangar, musamman ganin cewa; zanga-zangar ba za ta taba haifar da da mai ido ba.
“Gwamnatin Kaduna, ba ta goyon bayan wannan zanga-zanga; hasali ma, mun yi Allah wadai da ita; sakamakon lura da cewa, akwai makarkashiya a cikinta; domin kuwa makiya kishin Arewa ne ke son kawo nakasu a cikin gwamnati”
“Mun ja hankalin dukkannin kungiyoyin siyasa a kan kauce wa shiga wannan zanga-zanga, sakamakon ganin babu wani alheri a ciki”, a cewar Mustapha.
Wadannan dalilai ne suka Rigasa, ya bukaci daukacin al’ummar Jihar Kaduna, su zama masu yunkurin samar da zaman lafiya; yana mai cewa, babu inda zanga-zanga ke haifar da wani ci gaba; illa koma baya ga ci gaban tattalin arzikin jiha da ma kasa baki daya.
Haka nan, wasu masu ruwa da tsaki da suka hada da Kungiyar Daliban Nijeriya ta Kasa da Kungiyar Kula da Hakkin Musulmai da sauran wasu kungiyoyi, sun yi mi’ara koma baya dangane da shiga wannan zanga-zanga da ake sa ran farawa a ranar 1 ga Agustan wannan shekara, kodayake daliban sun ce za sus a ido su ga abin da gwamnati za ta yi tukuna, idan har ta gaza duba bukatun da aka gabatar, to za su shiga zanga-zangar.
Da yake jawabi a wajen taron manema labarai na duniya a Legas, Shugaban Kungiyar Daliban Nijeriya ta Kasa; reshen Jihar Legas, Kwamared Alimi Lekan Idris ya ce; a halin da ake ciki yanzu, kungiyar daliban ta fahimci muhimmancin zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma tattaunawa mai ma’ana, musamman wajen cimma burinsu na bai-daya. Don haka, akwai bukatar nisantar dukkanin wani abu da zai kawo rudani ko tashin hankali a tsakanin al’ummar wannan kasa.
Haka zalika, ya bayyana gagarumar gudunmawa da ci gaban da aka samu a jihar, inda shugaban daliban ya ce; “Ba ma goyon bayan dukkanin wata zanga-zangar adawa a kan Gwamnatin Jihar Legas.”
A matsayin nuna goyon bayan daliban ga Gwamnatin Jihar Legas tare kuma da jajircewarsu wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, Idris ya ce; “Kungiyar daliban reshen Jihar Legas, za ta gudanar da tattaki na hadin gwiwa, domin nuna goyon baya ga gwamnatin jihar daga 1 zuwa 10 ga watan Augustan 2024, wato a daidai lokacin da ake gudanar da wannan zanga-zanga, wadda har yanzu ba san ko su waye suka shirya ba.”
Kungiyar daliban ta ce, ta fahimci takaici da kuma kalubalen da mutane da dama ke fuskanta, ta kara da cewa; “Dole ne mu fahimci ci gaba da damammakin da aka samar domin dakile tasirin tattalin arzikin wannan kasa.”
Don haka, Idris ya bukaci sauran gwamnatocin jihohi; da su yi koyi da Jihar Legas kan haka. Ya kara da cewa, kungiyar daliban ba za ta iya bayar da hadin kai wajen sake maimaita abin da ya faru a lokacin EndSARS ba, barnatar da abubuwa babu gaira babu dalili ba.
Shugaban daliban ya ci gaba da cewa, “Babu abin da muka sanya a gaba a halin yanzu, kamar kare tare da kiyaye zaman lafiya da ci gaban Legas.”
Ya kuma bukaci daukacin daliban, da su mayar da hankali wajen tattaunawa a kan abubuwa masu muhimmanci da suka hada da ayyukan sa kai, ayyukan ci gaban al’umma, shiga cikin shirye-shiryen dalibai da gwamnati da kuma neman karin karatu, don samun ingantaccen ilimi.
“Duk lokacin da aka yi hakuri tare da bai wa gwamnati hadin kai, za a samu saukin warware matsalolin da suke addabar mu a halin yanzu.”
“Bari mu tsaya tare cikin hadin kai da kuma manufa guda daya tare da tabbatar da cewa, ayyukanmu na nuna kudirinmu na samar da kyakkyawar makoma ga kowa da kowa,” Idris ya hori daliban.
Haka zalika, a jawabin da Shugaban Kasa Bola Ahmad Tunubu ya yi, ya ja hankali tare da yin kira ga matasan Nijeriya da su janye batun wannan zanga-zanga tare da jiran abubuwan da gwamnatin tarayyar ta tanadar musu.
A ta bakin Ministan Yada Labarai, Muhammad Idris ya bayyana cewa; Shugaba Bola Ahmad Tunubu, na da kyakkyawan tsari ga al’ummar wannan kasa baki daya, illa kawai dai yana da bukatar lokaci.
Ya kara da cewa, saboda damuwa da bukatar ‘yan Nijeriya, cikin kankanin lokaci; Tinubu ya amince da Naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi, sannan kuma; tuni majalisar tarayya ta amince da wannan kudiri nasa.
Yana mai cewa, “Wannan ya tabbatar da cewa, shugaban kasa ya damu matuka da matsalolin da ‘yan Nijeriya ke ciki. Don haka, ya bukaci al’ummar wannan kasa da su dakatar da shirin yi wa gwamnatin Tunubun zanga-zanga.
Bugu da kari kuma, Rundunar ‘Yansandar Jihar Kaduna, ta bayyana cewa; ta kammala shirinta tsaf wajen domin ko ta kwana, don dakile dukkanin wani yunkuri da zai iya haifar da rashin zaman lafiya a fadin jihar.
Hasali ma, Babban Sufeton Rundunar ‘Yan Sadan Nijeriya (IGP), Kayode Egbetokun ya ce; sun kammala shiryawa tsaf, domin tunkarar wannan zanga-zanga da wasu ‘yan kasa ke shiryawa a wata mai zuwa, yana mai cewa, “Za mu kare masu zanga-zangar matukar ta kasance ta lumana ce”.
Egbetokun, ya bayyana haka ne; a yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai, inda ya yi kira ga matasan da su yi hakuri da fitowa wannan zanga-zanga; dalili kuwa gwamnati na iya bakin kokarinta wajen magance matsalolin da suka addabi kasar, ya ce; “Za mu kare masu zanga-zangar matukar dai ta lumana ce”.
Sai dai, da yake magana bayan ganawa da manyan jami’an rundunar na fadin Nijeriya, Egbetokun ya yi kira ga matasa da su yi hakuri da zanga-zangar, “Sakamakon cewa, gwamnati na bakin kokarinta”.
“Idan zanga-zangar ta lumana ce, za ku gan mu muna kare masu yin ta. Ko kadan ba ma adawa da zanga-zangar lumana, za kuma mu taimaka wa masu zanga-zangar lumanan, saboda kuwa ‘yancinsu ne”, in ji shi.
A hannu guda kuma, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa; Atiku Abubakar, ya kalubalanci gwamatin tarayya da sauran hukumomi, bisa kokarin hana zanga-zangar da aka shirya a ranar 1 ga watan Agusta, a fadin wannan kasa.
Atiku ya kara da cewa, abin mamaki wai wadanda suka yi zanga-zanga a tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ne yanzu ke kokarin tauye wa wasu nasu ‘yancin na yin zanga-zanga.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta (facebook) a ranar Talata, Atiku ya ce hakki ne na ‘yan kasa su yi zanga-zanga, wanda kundin tsarin mulki ya ba su dama.
Gwamnatin ta san abin da take yi, ita ce, mai kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ‘yan kasa tare da ba su damar da kundin mulkin kasa ya tanadar musu na gudanar da zanga-zangar lumana.
“Don kauce wa shakku, ‘yancin ‘yan kasa na yin zanga-zanga na cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya kuma kotunanmu sun tabbatar da haka. Sashe na 40 na kundin tsarin mulki na shekarar 1999 (kamar yadda aka yi garanbawul), ya ba da tabbacin ‘yancin yin taron kungiyoyi na lumana.”
“Fakewa da yi wa masu yunkurin wannan zanga-zanga da rufa-rufa, aikin banza ne; musamman ganin cewa, ‘yan Nijeriya ciki har da magoya bayan Tinibu na Jam’iyyar APC; sun afka cikin yunwa da bacin rai da rashin yabawa kan iya aiwatar jagoranci da kuma sanin ya kamata a wannan gwamnati.”
“Dukkannin wani yunkuri na danne wadannan hakkoki, ba wai tsarin mulki kadai ya sabawa ba; illa dai kawai cin zarafi ne ga tsarin demokradiyyarmu”, in ji Atiku.