ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wasu Ɓata-gari Na Iya Amfani Da Zanga-zanga Domin Tada Zaune Tsaye – Minista

by Sulaiman
2 years ago
Zanga-zanga

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tana sane da cewa, wasu mutane na son yin amfani da zanga-zangar da ake shirin yi wajen tayar da tarzoma kan ‘yan Nijeriyar da ba su ji ba ba su gani ba.

 

Ya ce, duk da yake gwamnatin Shugaba Tinubu ta amince da ‘yancin kowane ɗan Nijeriya na gudanar da zanga-zanga, ta duƙufa wajen ganin cewa waɗannan ayyuka ba su kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ko take haƙƙin wasu ba.

ADVERTISEMENT
  • Gwamnati Ba Za Ta Yi Amfani Da Karfi Ba Akan Masu Zanga-zanga – Minista
  • Zanga-zangar Matsin Rayuwa: Gwamnoni Sun Gana Da Ribadu Kan Sha’anin Tsaro

Idris ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Charismatic Bishops a wata ziyarar ban-girma da suka kai ofishin sa da ke Abuja a ranar Laraba.

 

LABARAI MASU NASABA

Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

A wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Watsa Labarai, Malam Rabi’u Ibrahim ya fitar, ministan ya ce: “Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta amince da ‘yancin kowa da kowa a cikin tsarin doka ya yi abin da yake ganin ya dace a gare shi. Don haka Shugaban Ƙasa ba ya adawa da kowace irin zanga-zanga amma Shugaban Ƙasa na adawa da tashin hankali da duk wani abu da zai taɓa lafiyar ‘yan Nijeriya.

 

“Ya yi imani kuma ya kasance yana cewa a cikin tsarin dimokiraɗiyya, kuna da ‘yancin yin duk abin da kuke so idan har wannan haƙƙin bai take haƙƙin wani ba.

 

“Dalilin da ya sa kowa yake taka-tsantsan kuma ya gaji da wannan zanga-zangar ta ƙasa saboda mun ga abin da ya faru a wasu ƙasashen ne. Mun san cewa da wuya a gudanar da wannan zanga-zangar kuma a samu zaman lafiya. Ba za mu yarda da hakan ba saboda wasu mutane suna jira su ɗauki doka a hannun su ”

 

Idris ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana da cikakkiyar masaniya game da damuwa da ƙorafe-ƙorafe da ‘yan Nijeriya ke yi a faɗin ƙasar nan, kuma ya himmatu wajen aiwatar da ingantattun manufofi da nufin magance matsalolin da ‘yan ƙasa ke fuskanta da kuma kawo sassauci ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya.

 

Ministan ya ce a wani mataki da ba a taɓa ganin irin sa ba, Shugaba Tinubu yana tsara tsarin biyan alawus-alawus ga dukkan matasan da suka kammala karatu a jami’a da kwalejin kimiyya da fasaha kafin su samu aikin yi.

 

Ya ce: “Kuma bayan haka, akwai wani sabon tsari da Shugaban Ƙasa ya yi, wanda za a fara ganin sa nan ba da daɗewa ba, wato duk matasa maza da mata da suka kammala jami’a da kwalejin kimiyya da fasaha kuma suna da takardar shaida kuma sun yi bautar ƙasa (NYSC) ba su samu aikin yi ba, za su samu wani abu daga gwamnati da za su ci gaba da rayuwa har sai lokacin da suka samu aikin yi.”

 

Ya bayyana cewa saboda jajircewar da Shugaban Ƙasar ya yi wajen kyautata rayuwar ma’aikatan Nijeriya, ko da kwamitin da ke kula da mafi ƙarancin albashi na ƙasa ya kammala aikin sa tare da miƙa rahoton sa, shugaban ya ci gaba da tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago har sai da aka cimma matsaya na mafi ƙarancin albashi na ƙasa naira 70,000.

 

Idris ya ce ɓullo da shirin iskar gas na CNG da Shugaban Ƙasa ya yi yana kawo sauyi a tattalin arzikin ƙasar saboda yadda ya rage kuɗin sufuri da kusan kashi 60.

 

Ya kuma bayyana irin cigaban da aka samu a harkar tsaro, inda ya ce tun zuwan gwamnatin Tinubu, an samu gagarumin cigaba a mafi yawan wuraren da ake tashe-tashen hankula, musamman a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

 

A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Charismatic Bishops, Archbishop Leonard Kawas, ya nesanta ƙungiyar da shirin gudanar da zanga-zangar, yana mai cewa wasu ƙungiyoyi sun tuntuɓe su domin shiga zanga-zangar.

 

Ya ce: “Mai girma Minista, a kwanan baya mun samu wasu kiraye-kiraye daga wasu ƙungiyoyin addini da sauran ƙungiyoyi suna neman mu shiga cikin shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan, wanda za a fara daga ranar 1 ga Agusta, 2024.

 

“Mun zo nan ne domin mu sanar da kai cewa ba ma tunanin haka. Mun gwammace mu yi kira da a yi sulhu.

 

“Mun yanke shawarar mu yi roƙo da a zauna lafiya tare da neman ’yan’uwan mu da aka yi wa ba daidai ba ta kowace hanya, su ba mu lokaci mu ci gaba da tattaunawa da wannan gwamnati a kan abubuwan da suka shafe su.”

 

Ya ce bayan Taron Coci na 2024, sun yanke shawarar yin haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya wajen yin addu’o’i da bayar da shawarwari domin samun nasarar gwamnatin Tinubu.

 

Archbishop Kawas ya tabbatar da cewa gwamnatin ta samu gagarumin cigaba a fannin zuba jari a cikin al’umma, ɓullo da Shirin Lamuni na Ɗalibai, tsaro, samar da ababen more rayuwa a Babban Birnin Tarayya, da kuma ƙaddamar da mafi ƙarancin albashi na naira 70,000, da dai sauran su.

 

Har ila yau, Ƙungiyar Charismatic Bishops ta yi amfani da ziyarar ta ba da lambar yabo ta hidima ga Minista Idris.

Zanga-zanga
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya
  • Sulaiman
    Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030
  • Sulaiman
    Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara
  • Sulaiman
    Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

MASU ALAKA

Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano
Labarai

Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

July 17, 2026
An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi
Labarai

An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

July 17, 2026
Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara
Rahotonni

Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

July 17, 2026
Next Post
Zanga-zanga: Tinubu Ya Yi Taron Gaggawa Da Manyan Sarakunan Gargajiya A Abuja

Zanga-zanga: Tinubu Ya Yi Taron Gaggawa Da Manyan Sarakunan Gargajiya A Abuja

LABARAI MASU NASABA

Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

July 17, 2026
Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

July 17, 2026
Gwamnan Da Bai Taba Samun Mulkin Jihar Kano Ba

Gwamnan Da Bai Taba Samun Mulkin Jihar Kano Ba

July 17, 2026
An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

July 17, 2026
NPA Ta Tara Kudin Shiga Naira Biliyan 758.2 A 2024

Dalilin Da Ya Sa Kungiyar NCTR Ta Jinjina Wa Shugaban NPA

July 17, 2026
Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

July 17, 2026
Gbajabiamila Ya Maka Daraktan Bogi Na PFIPC Kotu, Ya Nemi Diyyar Biliyan 15

Gbajabiamila Ya Maka Daraktan Bogi Na PFIPC Kotu, Ya Nemi Diyyar Biliyan 15

July 17, 2026
Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

July 17, 2026
Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

July 17, 2026
Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

July 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.