An fito da kura-kuren da ake samu wajen fassarawa ko rubuta labarai a gidajen rediyo da telbijin na kasar nan a taron da cibiyar nazarin harsunan Nijeriya ta Jami’ar Bayero karkashin shugabancin Farfesa Yakubu Magaji Azare.
An dai gudanar da taron ne a harabar tsohowar jami’ar Bayero da ke Jihar Kano.
- Tinubu Ya Gana Da Gwamnonin APC Kan Zanga-zangar Matsin Rayuwa
- Ƴancin Gashin Kai: Gwamnati Ta Gargadi Ƙananan Hukumomi Kan Kashe Kuɗaɗensu
Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki kan fassara, malaman jami’a, ma’aikatan gidan rediyo, ‘yan jaridu da kuma masu fassara a kotunan shari’ar kasar nan, domin inganta al’amuran fassara a wannan lokaci.
Taken taron dai shi ne, “Nasarori da kalubalen fassara”, wanda aka tattauna lamarin domin lalubo hanyar samun ingantaciyar fassara da ya kamata a rika yi a hanyoyin sadarwa na rediyo da talbijin, wanda a nan ne aka fi samun kura-kurai sabanin jaridu da suke kokari wajen yin kyakkywar fassara da kaucewa kura-kurai kamar yadda ake samu a rediyo da talbijin.
A jawabinsa, masanin harshen Hausa, Farfesa Hafiz Miko Yakasai yana da ra’ayin a daina kiran gidajen rediyo da talbijin da jarida da sauransu a matsayin kafofin watsa labarai, don haka hanyoyin sadarwa shi ne, wanda ake yin daidai a fahimtarsa da ra’ayinsa a matsayinsa na farfesa a harshen Hausa.
Shi kuwa ma’aikacin gidan rediyon Premier, Malam Aliyu Abubakar Getso, ya ce akwai kura-kurai masu yawa da ake yi wajen fassara ko rubuta labarai, inda ya ba da misisali da wasu ‘yan jarida masu cewa, ‘‘yan takarkaru’, wanda kuskure ne sai dai a ce, ‘yan takara, shi ne daidai.
Shi ma tsohon shugaban kungiyar ‘yan jaridu na kasa kuma shugaban gidan rediyon Nasara, Malam Ismail Mai Zare, ya ce kuskure ne babba da masu fassara ko ‘yan jaridu ke yi wajen ba da labari ka ji an ce filin sauka da tashin jirgin sama na Malam Aminu Kano, ko na Murtala Muhammad, maimakon a ce filin saukar jirgin sama shi ne daidai.
A nasa bangaren, Farfesa Abdullah Uba, (FYD) ya ce wajibi ne a rika la’akari da harshen da mutanan gari suke yi da sauran bayanan matasa, musamman rubutu a kafofin sadarwa na zamani wato ‘Social Media’ da sauransu.
Malam Abubakar Adamu Rano, shi ne shugaban gidan rediyon Kano mafi dadewa a tsakanin gidajen rediyon Arewa, wanda aka kafa a 1946, ya ce su a matsayinsu na masu kyankyashe ma’aikatan rediyo da ake da su sama da 30 a Kano, to suna taka-tsantsan sosai na ganin sun bi ka’idojin aikin fassara da rubuta labari kamar yadda masana a wannan cibiya ta Jami’ar Bayero suke ilmantarwa.
Tun da farko a jawabinsa, mataimakin shugaban jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Farfesa Sani Muhammad Gumel ya bayyana cewa wannan taro abin farinciki ne kuma abun a yaba wa mahalartansa ne.
Ya ce ya kamata a sani cewa jami’a ba wurin karatu ba ne kawai, jami’a wani muhimmin wuri ne na canza rayuwar al’umma, don haka ne ma Jami’ar Bayero ta kasance mai cibiyoyi daban-daban kamar na CDA cibiya mai bincike kan gano iri da sauran abun da zai bunkasa harkokin noma dan samar da abinci a kasa ga kuma cibiya mai kula da al’amuran lafiya da dai sauransu a jami’ar.
Shugaban cibiyar nazarin harsunan Nijeriya na jami’ar Bayero, Farfesa Yakubu Magaji Azare ya ce dole ne mai fassara ya yi la’akari da al’adu da addini da shekaru mutane da sauransu.
Ya ce fassara ta kasu kasha-kashi, akwai fassara ta lokaci, akwai fassara nan take da dai sauransu, sannan a ilimance kuma wannan cibiya ta sha alkashin fito da dinbin rubuce-rubucen da aka yi na fassara na masana daban-daban da cibiyar take jibge, haka kuma a kwai yunkuri na shirya wani gagarimun taro wanda zai hada daukacin masu ruwa da tsaki kamar ‘yan jaridu, masana, malaman addini da sauransu, domin fito da gundarin harkar fassara ingantaciya.