Kasar Sin ta ce a shirye take gabatar da gogewarta wajen cimma zamanantar da kanta da kara inganta hadin kai da kasashen Afrika.
Mataimakin shugaban kwamitin din-din-din na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Li Hongzhong, ne ya bayyana haka a jiya, lokacin da yake jawabi ga bikin bude taron dandalin jama’ar Sin da Afrika karo na 7 da dandanlin shugabannin matasan Sin da Afrika karo na 7, wanda aka yi a Changsha, babban birnin lardin Hunan na tsakiyar kasar Sin.
- Sin Na Ci Gaba Da Ingiza Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
- Sin Ta Samu Karuwar Mafi Yawan Hatsi A Yanayin Zafi A Cikin Shekaru 9
Li Hongzhong ya kara da cewa, Sin za ta kara hada hannu da al’ummar Afrika da jam’iyyun siyasa na nahiyar domin zurfafa musaya da kara goyon bayan juna da neman ci gaba da inganta zaman lafiya da wayewar kai, ta yadda za a samar da yanayi mai kyau ga bangarorin biyu, wanda zai kai su ga cimma burikansu na samun ci gaba.
Tarukan biyu sun samu mahalarta sama da 200 daga kasashen Afrika sama da 50, ciki har da ‘yan siyasa da wakilan jam’iyyu da shugabannin matasa da wakilan kungiyoyi da kuma masana. (Fa’iza Mustapha)