Assalamualikum masu karatu barkanmu da sake haduwa da ku cikin wannan mako a shirinmu na Girki Adon Mace. Yau mun kawo muku tsarabar yadda ake Alale Mai Kwai
Abubuwan da ake bukata  su ne:
Wake, tattasai, attarugu, albasa, kwai, crayfish, manja, curry, da thyme, maggi
Da farko za ki wanke kwanki ki saka ta kan wuta ta tafaso, bayan kin saka sai ki kawo waken ki sai ki wanke ki cire bayan shi. Kayan attarugu da tattasai da albasa suma ki wanke su ki gyara ki hada wuri daya sai ki kai markade, amma idan kina da blender za ki iya yi a gida. Bayan nan za ki kawo manjanki da crayfish, thyme da curry da maggi ki zuba su cikin markaden sai ki motsa har sai ko ina ya samu. Sai ki kawo kwanki da ya nuna ki yanka shi daidai yadda ya yi miki.
- Matsin Da Karancin Abinci Ke Kara Haifarwa
- An Baro Shiri Tun Rani Game Da Shigo Da Abinci Ba Tare Da Biyan Haraji Ba
Leathern Alallen ki za ki zuba markadadden wakenki ciki sai ki dauki kwai ki saka a ciki, idan kin gama sai ki jera shi cikin tukuya ki saka masa ruwa kaman kofi daya ki rufe har sai ya nuna. Ana iya ci da Sauce ko kuma soyayyen manja da yaji, shikenan kin kammala.
A ci lafiya