Kawo yanzu ana ganin a Nahiyar Turai da duniya baki daya babu matashin dan wasa kamar Lamine Yamal, dan wasan Barcelona wanda tauraruwarsa ta haska a gasar cin kofin Nahiyar Turai da kasar Spaniya ta lashe.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta tabbatar da cewa dan wasa Lamine Yamal zai saka riga mai lamba 19 a kakar wasa ta 2024 zuwa 2025 a kungiyar, lambar da Patrick Kluibert da Leo Messi da Sergio Aguero suka yi amfani da ita a baya.
- Wa Zai Lashe Ballon d’Or Na Bana?
- Bach Ya Gode Wa CMG Bisa Kyakkyawar Shirin Da Ya Yi Don Watsa Wasannin Olympics
Dan wasan zai bi sawun fitattun ‘yan kwallon kungiyar da suka taka rawar gani a Barcelona, kuma lambar da ya yi amfani da ita kenan a gasar Euro 2024 a tawagar Sifaniya.
Sifaniya, wadda ta lashe gasar Euro 2024 ta dauki kofi na hudu jimilla, babu wadda ta dauki kofin da yawa kamarta, kuma Yamal ne matashin da ya yi fice a wasannin da aka yi a Jamus.
Dan wasa Bitor Rogue ne ya saka lamba 19 a bara a Barcelona, kuma lamba ce da matasa da yawa da fitattun da suka yi amfani da ita tun daga 1995.
Jerin wadanda suka yi amfani da lamba 19 a Barcelona:
Lluís Carreras (1995/96) – Juan Antonio Pizzi (1996-98) Patrick Kluibert (1998/99) Dani Garcia Lara (1999-03) Fernando Nabarro (2004/05) Leo Messi (2005-08) Madwell (2009-12) Martín Montoya (2012/13) Ibrahim Afellay (2013/14) Sandro Ramírez (2015/16) Lucas Digne (2016-18) Munir El Haddadi (2018) Kebin-Prince Boateng (2019) Carles Aleñá (2019) Martin Braithwaite (2020) Matheus Fernandes (2020/21) Kun Aguero (2021) Ferran Torres (2022) Franck Kessie (2022/23) Bitor Rokue, (2023/24).
Lamine ya cika shekara 17 da haihuwa ranar 13 ga watan Yulin 2024, ya saka riga mai lamba 27 a bara a Barcelona kuma a karkashin koci, Dabi Hernandez a kakar wasa ta 2023 zuwa 2024 ya buga wasa 50, inda Ilkay Gündoğan ne kan gaba a yawan yi wa kungiyar wasanni a bara inda ya yi wasanni 51.