Jiya Asabar, 27 ga watan nan, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana matsayin kasarsa kan batun tekun kudancin kasar Sin, yayin jerin tarukan ministocin harkokin waje kan hadin gwiwar kasashen gabashin Asiya da aka gudanar a birnin Vientiane na kasar Laos.
Wang Yi, ya bayyana cewa, mulkin kai da hakkin ruwa da kasar Sin ke da shi a tekun kudancin kasar, suna da isasshen tushe na tarihi da shari’a. Kasar Sin ta rattaba hannu kan sanarwar gudanar da ayyuka ta bangarori daban daban a tekun kudancin kasar Sin tare da kasashen ASEAN, bisa la’akari da kiyaye dangantakar abokantaka da kasashe makwabta, da hadin gwiwa a shiyyar. Kana ta aiwatar da sanarwar a kai a kai, tare da tsayawa tsayin daka kan kawar da bambance-bambance ta hanyar tattaunawa, da tuntubar kasashen da abin ya shafa kai tsaye.
Kaza lika, Wang Yi ya bayyana cewa, tekun kudancin kasar Sin na daya daga cikin hanyoyin teku mafi aminci da kwanciyar hankali a duniya, kuma babu wata matsala dake akwai wajen bin yankin, da ma wucewa ta samaniyar yankin. To sai dai kuma akwai fargabar wasu kasashen da ke wajen yankin na yunkurin haifar da hargitsi, da tada rikici a ko ina, har ma da yunkurin kai matsakaitan makamai masu linzami zuwa yankin, da haifar da arangama, wanda hakan ya kasance babban dalilin da ka iya lalata zaman lafiya a yankin tekun kudancin kasar Sin. (Bilkisu Xin)