Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa, mai taken ‘Take It Back Movement’, ya sha alwashin ci gaba da gudanar da zanga-zangar a dandalin Eagle Square da ke Abuja, ko gwamnati ta amince ko bata amince ba da amfani da dandalin.
Daraktan kungiyar, Damilare Adenola, wanda ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da kamfanin talabijin na Channels TV’s Sunday Politics, ya ce, an rubutawa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike don neman izini.
- Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Naɗa Sabon Kwamitin Gudanarwa Na Ƙungiyar Kano Pillars FC
- Ku Sha Kurumunku, Tinubu Zai Shawo Kan Matsalar Tattalin Arziƙin Nijeriya – Minista Harkokin Matasa
Shugaban matasan ya rattaba hannu kan wata wasika da aka aike wa ministan, inda ya nemi a yi amfani da wurin.
Wasikar dai ta kasance mai kwanan wata 26 ga Yuli, 2024, kuma an watsa ta a shafukan sada zumunta.
Sai dai har zuwa ranar Asabar din da tagabata, ministan ya ce, bai samu wasikar ba.
Amma Adenola a ranar Lahadi, ya dora alhakin jinkirin isar da wasikar a kan kura-kurai a cikin gwamnati amma ya ce, ba tare da kasa a guiwa ba, ministan zai samu wasikar a ranar Litinin.