Sojoji sun mamaye babbar hanyar da ta shiga babban birnin tarayya (FCT) kwanaki kafin gudanar da zanga-zangar da aka shirya domin nuna damuwa kan matsalar tattalin arziƙin da za a yi ranar 1 ga Agusta. Wannan sabon tsari, wanda ya fara a yau Litinin, ya haifar da cunkoson ababen hawa da kuma takaici ga masu bin hanya.
Sojojin sun kafa shingen binciken ababen hawa a kan hanyar Abuja-Keffe musamman a yankin Sani Abacha Barracks kafin gadar A-Y-A, wanda ya haifar da cunkoso har zuwa gadar Nyanya. Wannan shinge ya sa ma’aikatan gwamnati da ‘yan kasuwa da ke fita daga garuruwan da ke kusa irin su Nyanya, Karu, da kuma cikin jihar Nasarawa suka maƙale na tsawon sa’o’i.
- Zanga-zanga: Birtaniya, Amurka Da Kanada Sun Gargadi ‘Yan Kasarsu Mazauna Nijeriya
- Boko Haram Na Shirin Kutsawa Cikin Masu Zanga-zanga A Yobe – ‘Yansanda
Babu wata sanarwar da hukumomin tsaro suka bayar kafin wannan sauyi, masu amfani da wannan hanya sun sami kansu cikin dogayen layuka, inda wasu suka yanke shawarar komawa gida bayan sun kwashe sa’o’i da dama a cikin cunkoso.
A martanin da gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki suka yi dangane da zanga-zangar da ake shiryawa, sun yi kira ga masu shirya zanga-zangar su shiga tattaunawa maimakon gudanar da ita.
Ma’aikata sun nuna damuwa cewa zanga-zangar da ake shirin yi don nuna matsalolin tattalin arziki da ‘yan Nijeriya ke fuskanta, za a iya amfani da ita ta hanyar da za ta ƙara dagula yanayin tattalin arzikin ƙasar. Duk da wannan ƙoƙarin, matakin binciken ababen hawa da Sojojin suka ɗauka ya ƙara damuwa da tashin hankali a tsakanin al’umma.