Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya tabbatar da cewa dokar gyara domin samar da kuɗaɗe don cikakken aiwatar da sabon albashi mafi ƙaranci da aka sanya hannu a kai za ta tabbata a ranar Laraba, 31 ga Yuli, 2024.
Dokar ta na nufin yin gyara a kasafin kuɗin shekarar 2024 domin ware ƙarin Naira tiriliyan 6.2 don tallafa wa sabon tsarin albashi, wanda zai tabbatar da cewa ba wani ma’aikacin Nijeriya da zai rinka samun ƙasa da Naira 70,000.
- Majalisa Ta Amince N70,000 A Matsayin Sabon Mafi Karancin Albashi
- DA DUMI-DUMI: Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi Na Dubu 70
Akpabio ya jaddada cewa yana kira ga masu daukar ma’aikata su biya karin kuɗin idan suna da damar yin hakan.
Ya bayyana wannan gyaran a matsayin babbar ci gaba ga ma’aikatan Nijeriya, yana mai nuna cewa gwamnati tana da kudurin inganta walwalar su.
Farfesa Julius Ihonvbere, wanda ya yi magana a madadin Kakakin Majalisar Wakilai, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu saboda sanya hannu a kan dokar albashi mafi ƙarancin. Ya bayyana cewa wannan matakin yana nuna kulawar Shugaban ƙasa ga al’ummar Nijeriya da kuma kudurin gwamnatinsa na kai Nijeriya ga ci gaba mai ɗorewa da samun ingantacciyar rayuwa.