Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya ce Naira biliyan 900 da aka sake amince wa da su don yaki da rashin tsaro a kasar nan ba zai wadatar ba.
Lawan, yayin da yake jawabi ga ‘yan majalisar gabanin dage zaman majalisar domin tafiya hutu, ya koka kan yadda ‘yan ta’adda ke kashe rayukan da basu ji basu gani ba da kuma raunata ‘yan Kasar.
Ya ce, “ Kun sani cewa, abun nima ya dameni matuka kamar yadda ya da meku, mun tattauna sosai daku sosai a zamanmu na kebance da muka yi daku yau.
“Dole ne mu (Gwamnatin Tarayya) mu yi taka tsantsan kuma mu kula da alhakin da ya rataya a wuyanmu, musamman tabbatar da tsaro da kuma kare rayukan ‘yan kasarmu.
“Halin tsaro a ‘yan kwanakin nan na fuskantar kalubale, an samu karuwar hare-hare da kashe-kashe ga al’ummominmu.
“A matsayinmu na shuwagabannin al’ummarmu, alhaki ne akan mu a ko yaushe mu kare dukiyoyi da rayukan mutanenmu ta Hanyar bayar da duk abinda sojoji da hukumomin tsaronmu ke bukata.
“A baya, cikin kasafin Kudin Shekarar 2022, mun amince da Karin Kudi Naira Biliyan 900 ga hukumomin tsaro. Mun san cewa Karin kudin ba zai wadatar dasu ba, amma amincewa da Karin yana da muhimmanci matuka, kuma muna sa ran hukumomin tsaronmu za su yi aiki fiye da yadda suke yi a halin yanzu.”
Shugaban majalisar dattawan ya kuma sanar da ‘yan majalisar cewa za a iya kiransu a lokacin hutu domin su halarci abubuwan da ke faruwa a kasa idan bukatar hakan ta taso.