Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa (NAMA), ta dakatar da jiragen kamfanin Arik Air daga daukar fasinjoji bisa takaddamar bashin dala miliyan biyu da rabi da ake binsa.
Hukumar ta ce an dauki matakin ne bayan umarnin da babbar kotun tarayya a Abuja, ta bayar dangane da bashin dala miliyan 2.5 da kamfanin mai na Atlas Petroleum International Ltd. ke bin Arik Airline.
- An Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Hadin Gwiwa Tsakanin CMG Da AL
- Kiran Tada Hankali A Zanga-zanga: Rundunar ‘Yansanda Ta Cafke Wani Dan TikTok A Filato
“A ranar 19 ga watan Yuli, 2024, sashen aiwatar da doka na babbar kotun tarayya ya aiwatar da umarnin da kotun ta bayar game da bashin dala miliyan 2.5 da ake bin kamfanin Arik Airline ta hanyar karbe jiragensa,” a cewar wata sanarwa da NAMA ta fitar a ranar Talata.
“Kotun ta kuma sanar da Arik shirin yin gwanjon jiragensa a ranar 26 ga watan Yuli, 2024 kamar yadda kotun ta yi umarni idan suka kasa biyan bashin. Duk wadannan an sanar wa hukumarmu da kuma ministan sufurin jiragen sama.”
A cewar sanarwar, bayanai sun nuna cewa a ranar 8 ga watan Maris na 2016 ARIK ya daukaka kara a babbar kotun Jihar Legas, kuma a ranar 30 ga watan Satumban 2021 kotun ta yi watsi da daukaka karar tare da cin tararsa.
ARIK ya sake daukaka kara zuwa kotun koli ta neman izinin ya kara daukaka kara kan hukuncin, kuma a ranar 9 ga watan Janairun 2024, kotun koli karkashin Mai Shari’a Okoro, J.S.C. ta yi watsi da bukatar neman izinin sake daukaka karar.