Wani fitaccen Dan Boko Haram, Babakarami Balawan ya mika kansa ga sojojin Nijeriya a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno.
Balawan ya mika wuya ne biyo bayan hare-hare da dakarun sojojin suka kai maboyar ‘yan ta’addan da ke yankin.
- Boko Haram Na Shirin Kutsawa Cikin Masu Zanga-zanga A Yobe – ‘Yansanda
- Harin Boko Haram A Ofishin ‘Yansanda Ya Ci Rayukan Mutum Biyu Da Kone Motoci A Borno
Sojojin sun kashe wasu ‘yan ta’adda biyu tare da kwato bindiga kirar AK 49 guda daya da mujallun harsashi mai girman 7.62 na kungiyar tarayyar sojojin turai (NATO) ninki 11, da dai sauran harsashi na NATO.
Sanarwar da Rundunar Sojin Nijeriya ta fitar a shafinta na yanar gizo ta kuma bayyana cewa, sojojin sun ceto wata mata da ‘ya’yanta guda biyu a wani samame na ceto a karamar hukumar Gwoza ta jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp