A wani mummuna harin da aka kai a daren Lahadi, wasu ‘yan ta’addan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai farmaki ofishin ‘yansanda na Jakana da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno, inda suka yi sanadin mutuwar wani direban ‘yansanda da wata mata.
Maharan sun kuma kona motocin sintiri guda biyu na ‘yansanda da na Civilian Joint Task Force (CJTF), tare da wani babur, sannan suka sace makamai da alburusai.
- Muhimmin Sakon Kwankwaso Ga ‘Yan Nijeriya Kan Shirin Zanga-zanga
- Amfanin Hulba 21 Ga Lafiyar Dan’adam (2)
Jakana, tana da tazarar kilomita 45 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, kuma akan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
A cewar majiyoyin yankin, ‘yan ta’addan sun kai harin ne da misalin karfe 1 na dare, inda suka yi artabu da jami’an tsaro a wani kazamin fadan da ya dauki tsawon sa’oi kusan uku ana gwabzawa. Daga karshe ‘yan ta’addan suka ci karfin jami’an tsaron.
Shugaban karamar hukumar Konduga, Hon. Abbas Ali Abari, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilinmu.
Talla