An kashe wani mai zanga-zanga a Suleja a Jihar Neja, bayan wasu ɓata gari sun kwace zanga-zangar matsin rayuwa da aka yi wa laƙabi da #EndBadGovernance da ake yi a fadin kasar.
Zanga-zangar, wadda ta fara da mutum 25, ta rikiÉ—e zuwa tashin hankali bayan wasu ‘yan daba da aka fi sani da “Yangogoni” (Masu bin bola) sun tayar da hargitsi.
- Tsohon Ministan Buhari Ya Shiga Zanga-Zanga A Jos
- Masu Zanga-Zanga Sun Toshe Hanyar Abuja Zuwa Keffi
Marigayin ya mutu sakamakon raunukan da ya samu yayin rikicin.
Har yanzu ba a gano ainihin dalilin mutuwarsa ba a lokacin wannan rahoton.
Ana sa ran samun ƙarin bayani yayin da lamarin ke ci gaba da gudana.