Gwamna Dauda Lawal ya samu nasarar biyan haƙƙoƙin ‘yan fansho na Jihar Zamfara da na ƙananan hukumomi, fiye Naira Biliyan 7.
A watan Janairun wannan shekarar ne gwamnatin jihar Zamfara ta kafa wani kwamitin da zai tantance tsaffin ma’aikatan jihar da ba a biya su haƙƙin su na barin aiki ba, a tsakanin shekarar 2015 da 2024, da kuma bashin fanshon tsaffin ma’aikatan Ƙananan Hukumomi na tsakanin shekarar 2012 da 2019.
A cikin sanarwar da ya fitar yau a Gusau, Kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa ya zuwa yanzu an samu nasarar biyan bashin kuɗi N7,345,674,918.42 a biya bakwai da aka yi.
Sanarwar ta Sulaiman Bala ta ƙara haske da cewa wannan aiki na biyan basussukan tsaffin ma’aikatan, yana tafiya ba tare da wata tangarɗa ba.
Ya ce, “Gwamnatin jihar Zamfara a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta jajirce don ganin ta kammala biyan bashin tsaffin ma’aikatan jihar da na Ƙananan Hukumomi, wanda ya zarta Naira Biliyan 13.
“Abin takaici ne yadda gwamnatocin da suka gabata su ka bar tsaffin ma’aikatan cikin mawiyacin hali na ƙin biyan su haƙƙokin su na barin aiki, wanda alhamdu lillahi, yanzu Gwamna Lawal yana sallamar su.
“Yanzu dai waɗanda aka tantance su 1,926 cikin mutum 3,880 an biya su haƙƙoƙin su a biya bakwai da aka yi, wato kashi 1, 2, 3, 4, 5, da na 6, an biya su abin da ya kai ma tsabar kuɗi har N3,345,642,807.22, daga cikin N8,095,948,906.63 da ake bi.
“Kwanan nan ne aka biya kashi na bakwai, waɗanda suka kai su 215, wanda ya kai ma N499,886,578.77.
“A ɗaya ɓangaren kuma, an biya tsaffin ma’aikatan Ƙananan Hukumomi da Malaman makarantun Firamare su 3,513 a kashi bakwai, wanda ya kai ma N3,500,145,532.43.
“Za a ci gaba da wannan ƙoƙari, domin yana daga cikin shirin gwamnatin Zamfara na inganta harkar aikin gwamnati a jihar, don samar da ingantaccen aikin gwamnati.”