An shiga fargaba da fargaba a ranar Larabar da ta gabata a wasu manyan kasuwannin jihar Legas, yayin da ‘yan kasuwar suka rufe shagunansu tare da yi wa rumfunan yankar katin zabe na kananan hukumomi kawanya domin karbar katin zabe na dindindin kamar yadda shugabannin kasuwar suka umarce su gabanin zaben 2023.
Binciken LEADERSHIP ya nuna cewa an rufe kasuwannin ne don baiwa ‘yan kasuwa damar zuwa yin katin zabe.
- 2023: INEC Za Ta Rufe Rajistar Katin Zabe A Karshen Watan Yuli
- Fasinjoji 16 Sun Bace Sakamakon Nutsewar Kwale-kwale A Legas
’Yan kasuwar, musamman daga yankin birnin Legas da kewaye, sun yi wa cibiyoyin yankar katin kawanya, inda suka sha dukan rana da ruwan sama domin yin rajistar masu kada kuri’a.
Masu cin kasuwa da suka je kasuwar sayo kayan abinci da sauran kayayyaki a kasuwanni a fadin Legas sun fuskanci matsala wajen yin hakan inda ‘yan kasuwar suka sanar da su matakin da shugabannin kasuwar suka dauka na rufe kasuwannin na tsawon kwanaki biyu domin karbar katin zabe na dindindin kafin ranar ƙarshe.
A cewarsu, an dauki matakin dakatar da harkokin kasuwanci na tsawon kwanaki biyu a kasuwannin domin tabbar da yankar rajistar domin mambobinsu su samu su yanka gabanin cikar wa’adin ranar 31 ga watan Yuli da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanar. .
Wani dan kasuwa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an dauki wannan umarni na tara ‘yan kasuwar domin su samu katinan su na zabe a wani taron shugabannin kasuwar jihar karkashin jagorancin Iyaloja-Janar na Legas, Misis Iyabo Tinubu-Ojo.
“Iyaloja sun ce shugabannin kasuwar su hada kan ‘yan kasuwar su karbi katin zabensu, shi ya sa ba mu bude shaguna a yau ba. A gaskiya abin ya haifar da damuwa a kasuwanni saboda da yawa daga cikin ’yan kasuwa da masu saye ba su da masaniya kafin su zo kasuwa su sayar da kayayyaki,” inji shi.