Babban Sufeton Ƴansanda na ƙasa (IGP) Kayode Egbetokun ya ba da rahoton cewa an kashe wani ɗansanda yayin zanga-zangar da aka yi a fadin ƙasa a jiya Alhamis. A wani taron manema labarai, Egbetokun ya bayyana cewa an ji wa wasu jami’an Ƴansanda raunuka, kuma an lalata wasu ofisoshin Ƴansanda, a abin da ya bayyana a matsayin babbar tarzoma mai yawa.
Ya lura cewa zanga-zangar ta samu hare-hare marasa hujja akan jami’an tsaro a wurare kamar Abuja, da Kaduna, da Kano, da kuma Gombe. Saboda haka, Rundunar Ƴansandan Nijeriya ta sa dukkan sassanta a cikin shirin ko-ta-kwana, tare da tura jami’an masu yawa don tabbatar da doka da oda. Egbetokun ya jaddada buƙatar bin dokokin tsarin mulki yayin zanga-zanga kuma ya nuna yiwuwar amfani da sojoji don dawo da doka.
- Ƙarin Kuɗin Wutar Lantarki: Ƙungiyoyin Ƙwadago Sun Hana Shige Da Fice A Ofisoshin KAEDCO Da NERC A Kebbi
- Sakamakon Zanga-Zanga MTN Ta Rufe Ofisoshinta Na Kasar Gaba Ɗaya
Duk da cewa Egbetokun ya yi tsokaci kan abubuwan da suka shafi jami’an Ƴansanda da kayan aiki, bai tabo rahotannin da ke nuna cewa akwai asarar rayuka na fararen hula a wasu jihohi ba da babban birnin tarayyar ba.