Duk da dokar hana fita ta sa’o’i 24 da gwamnatin Jihar Jigawa ta saka, daruruwan matasa sun fita kan tituna a sassan Dutse, babban birnin jihar.Â
Gwamnati ta ayyana dokar hana fita bayan tashe-tashen hankula da barna a ranar farko ta zanga-zanga a kasar baki daya.
- Manzon Musamman Na Xi Jinping Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Kasar Mauritania
- Rahoton Zanga-zangar Yaƙi Da Fatara Da Tsadar Rayuwa A Nijeriya A Rana Ta 1
A halin yanzu hukumomin tsaro na fafatawa da masu zanga-zangar a kewayen yankin Zai na birnin.
A cewar daya daga cikin mazauna yankin na Zai, jami’an na kokarin hana matasan hawa shingayen hanya amma matasan sun tirje.
A Shuwarin da ke wajen birnin Dutse, matasa sun sake haduwa tare da ci gaba da zanga-zanga a rana ta biyu.
Masu zanga-zangar na kokarin shiga manyan sassan babban birnin jihar amma jami’an tsaro na kokarin hana su.
Wani ganau a Shuwarin ya ce ‘yansanda sun kama dubun-dubatar matasa da suka hada da yara masu matsakaitan shekaru.
A garin Gumel, lamarin ya kasance cikin kwanciyar hankali yayin da jami’an tsaro suka toshe dukkan manyan tituna don hana masu zanga-zangar sake haduwa.
Kokarin samun karin bayani game da halin da ake ciki a wurare kamar Hadeji, Birnin Kudu, Jahun, da Kazaure ya ci tura sakamakon rashin kyakkyawan hanyar sadarwa ta wayar salula.