Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai ya yi barazanar korar dukkanin malamin jami’ar jihar Kaduna (KASU) da ya shiga yajin aikin da kungiyar Malaman jami’o’i (ASUU) ke kan yi a halin yanzu.
ASUU dai tun a watan Fabrairu ta shiga yajin aiki kan gaza cika musu bukatunsu daga wajen gwamnatin tarayya. An yi ta kokarin yadda za a yi domin shawo kan yajin aikin amma har yanzu babu wani sakamako mai kyau, inda ko a ranar Litinin ma kungiyoyin Kwadago suka gudanar da jerin gwano a kasa baki daya domin mara wa ASUU ba.
- ASUU Ta Soki NLC Kan Yin Zanga-Zangar Minti 20 A Anambra
- Da Dumi-Dumi: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Barazanar Sace Buhari Da El-Rufai
Da ya ke magana cikin wani shirin rediyo a Kaduna a ranar Larabar, el-Rufai ya bukaci malaman da su koma ajuzuwansu domin ci gaba da koyar da dalibai domin kauce wa rasa aikinsu.
Gwamnan ya ce malaman KASU ba su da wani dalilin shiga wani yajin aiki. Ya kara da cewa ASUU na da matsalolin ne da gwamnatin tarayya ba da jihar ba.
“Mukaddashin Shugaban Jami’ar ya tabbatar min da cewa za su koma bakin aiki na kuma nemi su tabbatar da sun koma din domin da farko na bada umarnin a dakatar da biyansu albashi. Na umarci a bincika duk wanda ya karbi albashi kuma ya shiga yajin aiki dole ya dawo da albashin da ya karba.”
“Saboda dokar Nijeriya ya ce babu aiki babu biya. Don haka wannan dokar. Don haka duk wanda ya shiga yajin aiki to babu batun biyanshi albashi. Mun sha fada wa malaman KASU cewa ba su da wata matsala da gwamnatin Jihar Kaduna. Matsalar ASUU matsala ce da gwamnatin tarayya, don haka don meye ma’aikatanmu da ba su da matsala da mu za su shiga yajin aiki.
“Idan hakan ya ci gaba da faruwa, rana daya zan tashi na kori dukkaninsu. Na rantse da Allah. Za mu kori dukkaninsu kuma mu sanar da bukatar daukar ma’aikatan da za su maye gurbinsa a shafukan jaridu. Da zarar suka sake yin irin wannan bayan gargadin da muka ba su. Na rantse da Allah zan kori dukkanin wadanda suka shiga yajin aiki da kin komawa bakin aiki.”