Wani da ake zargin Barawo ne ya gamu da ajalinsa ranar litinin da ta gabata yayin da katangar da yake kokarin haurawa ya shiga wani gida ta fado masa aka.
Lamarin ya faru ne a wata unguwa da ake kira da Bagadaza a cikin garin Gombe lokacin da mutumin da ake zargin mai kimamin shekaru 38 ya yi kokarin hayewa ta katangar wani gida don yin sata bayan ya tarar da kofar da tagogin gidan a kulle.
- Goje Ya Raba Taki Na Naira Miliyan 300 Ga Manoman Gombe
- Gwamnan Gombe Ya Yi Alhinin Rasuwar Sheikh Maigano Da Ya Rasu A Saudiyya
Gidan dai na wani dattijo ne da ake kira Hashimu Ali. Wadanda abun ya faru a idonsu sun bayyana wa wakilinmu cewa ‘yan unguwar sun wayi gari bayan asubahi cikin mamaki lokacin da suka ga gawar mutumin a karkashin ginin daya rushe.
“Shima mai gidan bai san abunda yake faruwa ba sai bayan da yaji hayaniya a kofar gidansa, da ya fito ne ya tarar da abun da ya auku.
“Binciken da mu ‘yan unguwar muka gudanar, ya nuna cewa Barawon mazaunin unguwar Hausawa ne da ke Malori Pantami a cikin garin Gombe kuma magidanci ne mai mata biyu”. Cewar wasu ‘yan unguwar.
Jaridar LEADESHIP ta gano cewa da ‘yan unguwar suka ga haka, sun gayyaci ‘yan sanda don su dauke gawar Barawon.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandar jihar Gombe’ Mahid Mu’azu Abubakar, ya tabbatarwa da wakilinmu aukuwar al’amarin a ranar Laraba.