Ɗaruruwan masu zanga-zanga a Jos, Jihar Filato, sun fito kan tituna a yau Lahadi, suka mamaye hanyar zuwa Bauchi tare da gargaɗi ga masu kasuwanci a yankin da ko su shiga zanga-zangar gobe Litinin ko su rufe shagunansu domin guje wa yin ɓarna ga dukiyarsu.
Masu zanga-zangar sun nuna rashin jin daɗinsu da jawabin shugaban ƙasa Bola Tinubu na ranar Lahadi, suna masu cewa bai magance matsalolin da ke addabar ƙasar ba.
- Akwai Raɗaɗi Da Zafi Kan Cire Tallafin Man Fetur Amma Ya Zama Dole – Tinubu Ga masu Zanga-zangar
- Masu Zanga-Zanga A Kano Na Neman Taimakon Ƙasar Rasha
Rike da alluna, da ganye, da tutoci na ƙasashe daban-daban, masu zanga-zangar suka yi ta yawo a tituna daban-daban, suna kira ga kowa ya shiga zanga-zangar. Manyan buƙatunsu sun haɗa da dawo da tallafin mai da magance rashin tsaro a ƙasar.
Shugaba Tinubu, a cikin jawabin nasa, ya bayyana cire tallafin mai a matsayin wani mataki mai wuya amma da ya zama wajibi don cigaban tattalin arzikin ƙasa. Duk da ƙarin damuwa da ake fuskanta, zanga-zangar a Filato ta kasance cikin lumana, ba tare da samun rahoton tashin hankali ba.