Wata mummunar ambaliyar ruwa ta afkawa kasuwar Dodoru da ke ƙaramar hukumar Gwandu a jihar Kebbi, inda ta lalata shaguna da rumfuna sama da 51, Kasuwar wadda ita ce ɗaya daga cikin babbar hanyar samar da kuɗaɗen shiga ga jihar, tana jan hankalin dubban ‘yan kasuwa da kwastomomi daga sassan yankin a duk ranar Litinin.
Ambaliyar ruwan wadda ta afku a yau Litinin, ta bar Kasuwar cikin rugujewa, inda ‘yan kasuwa da dama suka yi asarar duniyoyinsu da kuma sauran wasu Kayayyakinsu na Miliyoyin Nairori.
Haka kuma kayan abinci, da wasu sassan kasuwar sun samu mummunar illa, inda buhunan taki, da gishiri, da sauran kayan amfanin gona suka lalace.
- An Yi Wa Matashi Daurin Rai Da Rai Kan Yi Wa Kurma Fyade A Kebbi
- Hukumar SEMA Ta Jihar Kebbi Ta Tallafa Wa Mutanen Da Ambaliyar Ruwan Sama Ta Shafa A Argungu
‘Yan kasuwa da kwastomomi suna ta kokawa game da ambaliyar, sakamakon asarar da mata tafka, kamar yadda wani dan Kasuwa wanda ya nemi a sakaye sunansa ya ce “Na yi asarar sama da buhunan gishiri 60 da sauran kayayyaki,” in ji wani ɗan Kasuwa. “Ban san yadda zan farfaɗo daga wannan halin ba.”
Shugaban ƙungiyar ‘yan Kasuwar, Alhaji Bello Aliyu Gwandu, ya roƙi gwamnatin jihar da ta taimaka wa ‘yan Kasuwa kan wannan ambaliyar ruwan da ta sanya ‘yan Kasuwarmu asarar dukiyarsu “Wannan Kasuwa ita ce jigon rayuwar al’ummarmu, muna buƙatar taimako don sake farfadowa,” inji shi.
Kasuwar Dodoru wani muhimmin bangare ne na tattalin arzikin yankin, inda ake samun kuɗaɗen shiga a kowane mako. Rushewarta zai haifar da rashin aiki da taɓarɓarewar tattalin arziki da asara mai yawa ga al’umma da kuma jihar.