Ana sa ran mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris, ta bayyana sunan wanda ta zaba a matsayin mataimaki takararta a ranar Talata.
Wannan na zuwa ne bayan da ta gana da masu takara a gidanta na birnin Washington a karshen makon da ya gabata.
- Duk Da Dokar Hana Fita, Matasa Sun Yi Fito Na Fito Da Jami’an Tsaro A Jos
- Sin Ta Gaggauta Raya Tsarin Yaki Da Balaun Ambaliyar Ruwa Da Fari
Harrisn, ta kammala neman da ta ke na mataimaki bayan da ta gana da wasu manyan ‘yan takara uku, wato gwamnan Jihar Minnesota, Tim Walz, sai Sanata mai wakiltar Jihar Arizona, Mark Kelly da gwamnan Pennsylvania, Josh Shapiro kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana.
Makonni biyu da suka wuce ne kawai Harris ta fara neman mataimaki, jim kadan bayan da shugaba Joe Bidn ya janye daga takarar shugabancin kasar, ya kuma zabe ta domin maye gurbinsa.
Zaben abokin takara na daga cikin matakan da za su fi yin tasiri a a harkar siyasarta, a yayin da ta ke hanzari wajen fara yakin neman zabe don kalubalantar tsohon shugaban kasar, Trump a ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Ilahirin mutanen da Harris za ta zaba mataimaki daga cikinsu fararen fata ne, wadanda suke da tarihin lashe zabe a inda fararen fata suka mamaye, da kuma masu zabe da ba su da jam’iyya.