Ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, ta gargadi ‘yan kasar da ke son zuwa Birtaniya hatsarin da ke tattare da kasar biyo bayan tashin-tashina da ake yi sakamakon zanga-zanga da ta barke.
Kakakin ma’aikatar ne, ya bayyana wannan cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
- Zanga-zanga: Tinubu Bai Damu Da Halin Da ‘Yan Nijeriya Ke Ciki Ba – PDP
- Tinubu Ya Ba da Umarnin Kame Duk Masu Ɗaga Tutar Rasha Yayin Zanga-Zanga
“Akwai karuwar tashin hankali da tarzomar da ake yi a Birtaniya, sakamakon kashe wasu ‘yan mata uku a wajen wani shagali.
“Lamarin ya rincabe zuwa tashin hankali ta hanyar kai hari kan jami’an tsaro da kuma lalata ababen more rayuwa.
“Don haka, an shawarci ‘yan Nijeriya da su yi taka-tsan-tsan tare da guje wa al’amuran siyasa da zanga-zanga.
“Ku guje wa cunkoson jama’a da manyan taruka, ku kasance masu neman bayanai.
“Ku ke tuntubar Hukumar da don neman karin haske game da bayanan da suka dace ta hanyar imel da kuma wayar tarho; +442078391244,” in ji shi.
Kakakin ya ce zanga-zangar da wasu ke yi a Birtaniya ta bar baya da kura, ta hanyar da ba ta dace ba, wanda hakan ya haifar da rudani a kasar.
Ya ce wadannan rikice-rikicen sun samo asali ne tare da rura wutar mutuwar ‘yan matan uku.